Shugaba Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan kare dimokuraɗiyya a Jamhuriyar Binin
Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar bisa gaggawar da ta yi wajen amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Binin domin taimakawa wajen kare tsarin mulkinsu na dimokuraɗiyya, bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar da safiyar Lahadi. A cewar fadar shugaban ƙasa, gwamnatin Binin ta aikawa Najeriya da buƙatu biyu na gaggawa,…
