Ashafa Murnai Barkiya
A matsayin sa na babban jigon kula da dukkan bankuna a Nijeriya, kuma jagoran bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bar adadin kashi 27% a matsayin kuɗin ruwa, daga kuɗaɗen da masu karɓar ramce za su amsa daga bankuna.
Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka, bayan tashi daga Taron Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗi (MPC) na Babban Bankin Najeriya (CBN), a ranar Talata, a hedkwatar bankin da ke Abuja.
Da yake ganawa da manema labarai, Cardoso ya ce CBN yana ci gaba da dakatar da ƙarin tsauraran matakai, domin bai wa manufofin baya damar fara aiki yadda ya kamata.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana haka a Abuja bayan kammala taron MPC na 303, inda ya ce yawancin mambobin kwamiti sun jefa ƙuri’a don ci gaba da tsare-tsaren manufofin kuɗi na yanzu, duk da kiraye-kirayen da masana’antu da ‘yan kasuwa suka riƙa yi kan a sassauta kuɗin ruwan, domin rage tsadar karɓar ramce a bankuna.
Wannan dai shi ne karo na huɗu a 2025 da aka bar adadin kuɗin ruwa a matakin da yake, bayan saukar ɗigo 50 kacal a watan Satumba, wanda shi ne saukin da aka yi bayan tsauraran matakai da yawa a 2024.
Wannan taro wanda shi ne na 303 a tarihin kafa CBN, kuma na ƙarshe a shekarar 2025, ya gindaya wa bankuna cewa tilas kowane banki ya riƙa ajiye kashi 45% na kuɗin sa a CBN, wato ‘Cash Reserve Ratio’ (CCR). Shi wannan adadin kuɗi ne da bankuna ke ajiyewa a CBN, ba tare da suna ɗiba daga ciki suna bayarwa ramce ko sayen hannayen jari da su ba.
Sai kuma geji da ƙarfin biyan basussuka a cikin gajeren lokaci, wato
‘Liquidity Ratio’, wanda ya tsaya a kashi 30% ɗin sa.
Cardoso ya ce wannan mataki na nufin “ƙarfafa nasarar da aka samu wajen rage hauhawar farashi.”
CBN ta bayyana cewa hauhawar farashi ya ragu a watanni bakwai a jere, ya sauka zuwa 16.05% a Oktoba daga 34% a bara.
Hauhawar farashin abinci ya koma 13.12%, yayin da na cikin gida ya ragu zuwa 18.69%.
An danganta wannan raguwar da tsauraran matakan kuɗi sakamakon daidaiton kasuwar canjin kuɗi, ƙaruwar masu zuba jari daga waje, da daidaiton farashin main fetur.
Ya sanar da cewa Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Waje ya ƙaru zuwa $46.7bn, daga $42.77bn a Satumba.
Cardoso ya danganta hakan da ƙaruwa a fitar da kayayyakin da ba na mai ba, ƙaruwar samar da yawan mai, ƙaruwa a kuɗaɗen shiga a Najeriya, sai kuma dawowar masu saka jari daga waje.
Ya kuma ce yanzu matafiya na iya yin amfani da katin naira a ƙasashen waje ba tare da takurawar da aka sani da ta gabata ba.
Alamomin Ci gaban Tattalin Arziki A Cikin Ƙasa:
Kwamitin MPC ya lura cewa Najeriya ta samu ci gaban tattalin arziki daga kayayyakin da sarrafawa a cikin gida, wato GDP na kashi 4.23% a watannin Afrilu, Mayu da Yuni, daga kashi 3.13% a farkon shekara.
Haka nan PMI ya tashi zuwa 56.4 a Nuwamba, mafi girma cikin shekaru biya, wanda haka yana nuna ƙarfafa harkokin kasuwanci musamman a ɓangaren da ba na mai ba.
Ya ce zuwa yanzu bankuna na ci gaba ƙoƙarin ƙarfafa jarin su. Har ya ce a yanzu haka bankuna 16 sun kammala, yayin da 27 ke cikin matakin ɗaga jari.
Maƙalewar Kuɗaɗen Tallafin Lamuni:
Cardoso ya bayyana cewa binciken cikin gida ya nuna an kashe Naira tiriliyan10.93 a tallafin da aka bayar a baya, inda har yanzu ba a kai ga ƙarni Naira tiriliyan 4.69 ba tukuna, waɗanda ba a biya ba.
.
Ya ce an amso yanzu ta dawo da Naira tiriliyan 2, amma ragowar ya na takure bankin wajen ɗaukar sabbin tsare-tsare.
Ya ce tsarin tallafin baya ya kawo tangarɗa da cikas a kasuwa, yana jaddada cewa yanzu CBN zai tallafa wa ci gaban tattalin arziki ta hanyoyi marasa samar da cikas a kasuwa.
Ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin hukumomin kuɗi da na gwamnati ya ƙara ƙarfi, wanda ya ce shi ne ginshiƙin da ya haifar da daidaito da ɗorewar tattalin arziki kan miƙaƙƙar turba.
