“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ba mutum ba ne wanda matsaloli ko ƙalubale suke firgita shi.
Tsarin sa a kowane lokaci ya kasance cikin natsuwa da yanke shawara—yana mayar da ƙalubale wata dama don yin abubuwa mafi kyau da inganci. Hulɗoɗin mu na baya-bayan nan da Amurka shaida ne.
A ƙarƙashin jagorancin sa, mun mayar da wani lokaci mai cike da tashin hankali wata dama ta ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu da kuma ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.”
-Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris
