Tinubu: Babu ja da baya kan janye ‘yan sanda daga rakiyar manyan jami’ai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai janye umarninsa na janye ‘yan sanda daga rakiyar Manyan mutane (VIPs), manyan jami’ai da ministoci ba, yana mai jaddada cewa wajibi ne a aiwatar da umarnin ba tare da wata tangarda ba.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a Abuja, yayin bude taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka gudanar a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa.

Tinubu ya gargadi duk wani minista ko jami’i da ke kokarin kauce wa umarnin, yana cewa duk wanda yanayin aikinsa ya bukaci kariyar ‘yan sanda, dole ne ya tuntubi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) tare da samun amincewarsa kai tsaye.

“Idan kuna da wata matsala saboda irin aikin da kuke yi, ku tuntubi IGP ku samu amincewata,” in ji Shugaban.

Shugaban kasar ya umurci Mai Bai da Shawara kan Tsaron ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Sanata Ibrahim Gaidam, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da su tabbatar an aiwatar da umarnin gaba ɗaya.

Ya bayyana cewa aikin ‘yan sanda shi ne kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, musamman masu rauni, ba wai kare rukunin VIPs da VVIPs ba.

Shugaban Tinubu ya kuma ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, zai shirya yadda Hukumar Tsaron Fararen Hula (Civil Defence Corps) za ta maye gurbin ‘yan sandan da ke aikin rakiyar manyan jami’ai.

“Hukumar Civil Defence na da horo na musamman kan kare VIPs, kuma suna dauke da makamai,” in ji shi.

Shugaban ya kara da cewa za a sake tsara tsarin tsaro domin fuskantar kalubalen satar mutane, ‘yan bindiga da ta’addanci, tare da tabbatar da an ba da kariya ga al’ummomi masu rauni.

Ya ce duk da cewa za a iya yin keɓantattun tanade-tanade a wasu lokuta, amma Civil Defence na da wadatattun jami’ai da za su iya cike gibin.

Shugaban ya kuma bukaci Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda shi ne Shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC), da ya kara wayar da kan gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki kan aiwatar da sauye-sauyen kiwon dabbobi ta hanyar kiwo na zamani (ranching).

Haka kuma ya umurci Ministan Kiwon Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha, da ya fara aikin tattara bayanai da aiwatar da shirin, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.

“A duba kauyuka ko wuraren kiwo da za a iya farfadowa domin kiwon zamani. Dole ne mu kawar da tushen rikici, mu kuma sanya gyaran kiwon dabbobi ya zama abin amfana ga tattalin arziki,” in ji Shugaban.

Tinubu ya jaddada cewa aiwatar da kiwo na zamani zai rage rikicin manoma da makiyaya, tare da kare rayukan al’umma, musamman masu rauni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *