Tinubu: Gwamnatin Najeriya Na Ci Gaba da Tattaunawa da Ƙasashen Duniya Ta Hanyar Diflomasiyya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na kan hanyar ci gaba da tabbatar da alaƙar diflomasiyya, yayin da manufofin tattalin arziƙin gwamnati ke fara haifar da sakamako mai gamsarwa a gida da kuma ƙasashen waje.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ranar Alhamis, bayan rantsar da sabbin ministoci biyu, Dr. Bernard Mohammed Doro da Dr. Kingsley Tochukwu Udeh (SAN). Doro zai jagoranci Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, yayin da Udeh zai rike Ma’aikatar Kirkire-Kirkire, Kimiyya da Fasaha.

Tinubu ya ce gwamnatin sa tana ci gaba da yin mu’amala da sauran ƙasashe ta hanyar diflomasiyya, duk da kalubalen siyasa da ake fuskanta.

Game da batun tsaro, Tinubu ya ce gwamnati ba za ta lamunci rashin zaman lafiya ba, yana mai tabbatar da cewa Najeriya za ta yaƙi ta’addanci gaba ɗaya.

“muna da matsaloli, muna fama da ta’addanci. Amma za mu ci nasara a kansu. Za mu tabbatar da an tsabtace ƙasar nan daga miyagun laifuka. Muna buƙatar abokanmu su taimaka mana, domin mu kawar da ta’addanci,” in ji shi.

A zaman majalisar, Shugaban Ƙasar ya umurci Ministan Kuɗi, Wale Edun, da ya gabatar da rahoton cigaban tattalin arziƙin ƙasar.

Edun ya bayyana cewa rahoton tattalin arziƙi ya nuna ƙaruwa sosai, inda ya ce ci gaban GDP na Najeriya ya kai kashi 4.23 cikin 100 a zangon na biyu na shekarar 2025, kaso mafi girma cikin shekaru goma.

Ya ƙara da cewa bangaren masana’antu ya kusan ninka ci gaban da ya samu daga kaso 3.72% zuwa kaso 7.45%, yayin da hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa kashi 18.02% a watan Satumba, kuma ajiyar kuɗin ƙasar ya kai dala biliyan 43.

“An kuma samu riba ta kasuwanci ta naira tiriliyan 7.4, alamar da ke nuna tattalin arziƙi na samun kwanciyar hankali. Yawan kuɗin da jama’a ke kashewa wajen abinci, sutura da zama ya ragu daga kashi 90 cikin 100 zuwa kusan rabin abin da ake samu, alamar cigaba daga rayuwar dogaro da kai zuwa ci gaban arziki,” in ji Edun.

Ya ce hangen nesan gwamnatin Tinubu na cimma tattalin arziƙin dala tiriliyan ɗaya nan da 2030 abu ne mai yiwuwa, muddin ana ci gaba da samun ci gaban kashi 7% a duk shekara.

Edun ya kuma bayyana cewa nasarar Eurobond da aka fitar jiya ta dala biliyan $2.35, wadda ta jawo buƙatar Naira ta sama da $13 biliyan, ta nuna yadda masu saka jari ke sake amincewa da shugabancin Tinubu da manufofin gwamnati.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da neman hanyoyin da za su tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, musamman ta hanyar haɗin gwiwa da jihohi don tabbatar da ayyuka masu amfani ga jama’a da jawo jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *