Tinubu ya ɗage tafiyarsa zuwa tarukan G20 da AU-EU saboda tattauna batun tsaro a ƙasar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya dage tafiyarsa zuwa tarukan shugabannin G20 a Johannesburg da kuma AU-EU a Luanda, domin ya samu karin bayanai kan matsalolin tsaro da suka kunno kai a jihohin Kebbi da Kwara.

A cikin wata sanarwa daga babban mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shugaban ya yanke shawarar dakatar da tafiyar ce sakamakon damuwarsa game da sace dalibai mata 24 a jihar Kebbi da kuma harin da ’yan bindiga suka kai wa mabiya addini a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, jihar Kwara.

A cewar sanarwar, Gwamnan Kwara ya nemi karin jami’an tsaro domin tunkarar kalubalen tsaro a yankin, kuma shugaban ya ba da umarnin a tura karin sojoji da ‘yan sanda zuwa Eruku da dukkan yankunan da ke cikin ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar.

Shugaba Tinubu ya kuma umurci rundunar ‘yan sanda da su bi diddigin wadanda suka kai harin, tare da tabbatar da cewa an kamo su.

An bayyana cewa shugaban kasa na jiran cikakken rahoton mataimakinsa, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, wanda ya ziyarci Kebbi domin jajantawa iyalan daliban da aka sace, da kuma rahotannin da ‘yan sanda da Hukumar DSS za su gabatar kan lamarin da ya faru a Kwara.

Shugaba Tinubu ya jaddada umarninsa ga hukumomin tsaro da su dauki duk matakan da suka dace domin ceto dalibai 24 da aka sace tare da dawo da su gida lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *