Tinubu ya naɗa Yakubu da ministoci shida a kwamitin warware bashin Naira tiriliyan 1.5 da ‘yan kwangila ke bin Gwamnatin Tarayya

Ashafa Murnai Barkiya

A ranar Laraba, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana rashin jin daɗi game da tarin bashin da gwamnatin tarayya ke bin ‘yan kwangila, tare da kafa wani babban kwamiti wanda ya ɗora wa gagarimin aikin magance matsalolin da ke hana biyan su da kuma samar da kuɗin biyan bashin.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a Abuja, Mashawarcin Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya ce Shugaban Ƙasar ya “ya nuna” bayan ya samu labarin cewa gwamnatin tarayya bin kusan ‘yan kwangila 2,000 bashi.

“Ya bayyana a fili ƙwarai cewa yana so a samu mafita guda ɗaya,” inji Onanuga. “Muhimmin abin da ya fito a taron FEC shi ne Shugaban Ƙasa ya nuna matuƙar rashin jin daɗi game da yadda ‘yan kwangila ke bin ɗimbin bashin da har yau ba a biya su ba.

“Daraktan Janar na Hukumar Kula da Sayar da Kadarorin Gwamnati (BPP) ya shaida wa Shugaban Ƙasa cewa ‘yan kwangila kusan 2000 na bin bashin kuɗaɗen ayyukan da suka yi. Don haka ministoci za su duba matsalar domin nemo mafita ta gaske da kuma kuɗin da za a yi amfani da su wajen biyan ‘yan kwangila,” ya ƙara bayani.

A Onanuga, kwamitin ya ƙunshi Ministan Kuɗi (kuma Mai Kula da Tattalin Arziki), Wale Edun; Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; Ministan Ayyuka, Dave Umahi; Ministan Ilimi, Olatunji Alausa; Ministan Gidaje, Ahmed Dangiwa; da Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku (Marine & Blue Economy), Gboyega Oyetola; tare da Daraktan Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Tanimu Yakubu; da Shugaban Hukumar Tara Harajiin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS), Zacch Adedeji.

“Dukkan su za su zauna su tsara shiri a matsayin kwamiti, su yi taro a matsayin kwamiti, sannan su je wajen Shugaban Ƙasa su gabatar masa da mafitar da suka samo wajen ware kuɗin da za a biya ‘yan kwangila,” inji shi.

Onanuga ya ƙara da cewa Daraktan Janar na BPP ya yi wa Majalisar bayani kan yawa da adadin bashin da aka gada, lamarin da ya sa Shugaban Ƙasa ya bayar da umarni.

“Manufar ita ce a nemo kuɗi a gyara matsalar biyan ‘yan kwangila. Dole ne mu duba matsalolin: Me ke jawo wannan matsala? Me ya sa FIRS ke cewa ana samun ƙarin kuɗaɗe, amma duk da haka ana bin ‘yan kwangila bashi? Me zai iya zama sanadin haka?

“Shi ya sa ya kafa kwamiti mai ministoci da dama domin duba matsalar. Har ma ya ce a matsayin ƙasa mai cikakken iko, za mu iya zuwa mu karɓo bashi domin biyan ‘yan kwangila. Amma ina ganin zuwa lokacin da mambobin kwamitin suka gana da shi yau, za a samu mafita,” cewa Onanuga.

Jawaban Onanuga sun biyo bayan makonni na matsin lamba daga ‘yan kwangila da suka koka kan jinkirin biyan bashin ayyukan da aka kammala tun cikin 2024.

A farkon watan Satumba, Ƙungiyar ‘Yan Kwangila ‘Yan Asalin Ƙasa ta Nijeriya ta yi zanga-zanga a Ma’aikatar Kuɗi a Abuja, tana iƙirarin cewa sama da Naira 4 na manyan ayyukan babban 2024 da aka tantance har yanzu ba a biya ba; adadin da aka kuma ambata yayin zanga-zangar su a Majalisar Ƙasa.

Ma’aikatar Ayyuka ta amince da tarin bashin tun da wuri, inda ta ƙaddamar da aikin tantancewa a watan Janairu 2024 domin warware kusan Naira tiriliyan 1.5 da ake bi na kwangilolin ayyukan ginin manyan titinan tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *