Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa kamfanonin Najeriya, ‘yan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwar hannun jari bisa nasarar da Kasuwar Musayar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX) ta kai darajar kasuwa ta Naira tiriliyan 100.
A cikin wata sanarwar fadar shugaban ƙasa da mai ba shi shawara na musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya ce wannan gagarumar nasara ta zama abin ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari a kasuwannin kuɗi da jarin ƙasa.
Shugaban ya ƙarfafi ‘yan Najeriya da su zuba jari a tattalin arzikin cikin gida, yana mai tabbatar da cewa shekarar 2026 za ta kawo riba mafi yawa yayin da gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatinsa ke ƙara haifar da sakamako mai ƙarfi.
Tinubu ya ce hayewar kasuwar Musayar Hannayen Jari Ta Najeriya (NGX) zuwa darajar Naira tiriliyan 100 alama ce ta sabon yanayin tattalin arziki da farfaɗo da kasuwar Najeriya. Ya bayyana cewa a shekarar 2025, duk da cikas da wasu kasuwannin duniya suka fuskanta, Alamar All-Share ta NGX ta tashi da kaso 51.19 cikin 100, fiye da kaso 37.65 na shekarar 2024, lamarin da ya sanya Najeriya cikin manyan kasuwanni masu riba a duniya.
Ya ƙara da cewa ribar da aka samu a bana ta zarce ta manyan kasuwannin duniya kamar S&P 500 da FTSE 100, har ma da wasu kasuwannin ƙasashe masu tasowa na ƙungiyar BRICS+, yana mai cewa Najeriya ba ƙasar da za a yi watsi da ita ba ce, illa wata ƙasa da ake gano ƙima a cikinta.
Shugaban ya nuna cewa kamfanoni da dama a dukkan fannoni sun nuna ƙwazo a NGX, daga manyan masana’antu da suka ƙarfafa samarwa a gida, zuwa bankuna da suka nuna juriya da ƙirƙira ta fasaha. Ya ce hakan na tabbatar da cewa kamfanonin Najeriya na iya samar da riba mai kyau ga masu zuba jari.
Tinubu ya kuma bayyana cewa ana sa ran ƙarin kamfanoni, musamman na makamashi, fasaha, sadarwa da manyan ayyukan more rayuwa, za su shiga kasuwar hannun jari, abin da zai ƙara darajar kasuwa da faɗaɗa mallakar tattalin arziki ga jama’a.
Game da gyare-gyaren tattalin arziki, shugaban ya ce bayan ƙalubalen farko, ana ganin saukar hauhawar farashi sakamakon tsauraran matakan kuɗi da dakatar da biyan “Ways and Means”, tare da bunƙasar zuba jari a noma. Ya ce hauhawar farashi ta ragu daga kashi 34.8 cikin 100 a Disambar 2024 zuwa kashi 14.45 cikin 100 a Nuwambar 2025, kuma ana hasashen ta kai kashi 12 a 2026, har ma ta faɗi ƙasa da kashi 10 kafin ƙarshen shekarar.
Tinubu ya ce ma’aunin asusun kasuwanci na ƙasa ya nuna ingantaccen yanayi, inda Najeriya ta samu rarar dala biliyan 16 a 2024, tare da hasashen kaiwa dala biliyan 18.81 a 2026. Ya ƙara da cewa fitar da kayayyakin da ba na mai ba ya ƙaru da kashi 48 zuwa Naira tiriliyan 9.2 a zangon uku na 2025, yayin da fitarwa zuwa Afirka ya tashi da kashi 97.
Shugaban ya kuma nuna cewa ajiyar kuɗaɗen waje ya wuce dala biliyan 45, tare da hasashen kaiwa dala biliyan 50 a farkon zangon 2026, yayin da Naira ta samu daidaito. Ya ambaci ci gaba a hanyoyin jirgin ƙasa, manyan tituna, tashoshin jiragen ruwa, da kuma manyan ayyukan superhighway na Lagos–Calabar da Sokoto–Badagry.
A cewar Tinubu, ana samun inganci a cibiyoyin kiwon lafiya, raguwar kuɗin yawon neman magani a ƙasashen waje, tallafin lamunin ilimi na NELFUND, da ƙarin tallafin bincike ga jami’o’i.
Ya kammala da cewa gina ƙasa tsari ne mai ɗaukar lokaci, inda Naira tiriliyan 100 ta zama saƙo ga duniya cewa tattalin arzikin Najeriya na da ƙarfi. Ya yi alƙawarin ci gaba da aiki tuƙuru wajen gina tattalin arziki mai daidaito, gaskiya da bunƙasa, tare da aiwatar da manyan gyare-gyaren haraji da kuɗi da suka fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
