Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa dawo da zaman lafiya, ƙarfafa tsaron ƙasa, da faɗaɗa damar tattalin arziki su ne manyan abubuwan da gwamnatin sa ta fi mayar da hankali a kai.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a madadin Shugaban, a lokacin taron tunawa da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, marigayi Yarima Abubakar Audu a Lokoja ranar Lahadi.
Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya sosai don fatattakar dukkan maƙiyan ƙasa ko ina suke domin dawo da zaman lafiyar da kowane ɗan Nijeriya ke da haƙƙin gadon sa.
Ya ce: “Amma ba mu yaudari kan mu game da ƙalubalen tsaro da matsalolin baya-bayan nan da suka gwada ƙarfin gwiwar ƙasar mu ba. Bari in fayyace: tsaro da walwalar kowane ɗan Nijeriya su ne muhimman abubuwan da gwamnati na ta ɗauka matsayin muƙami mai tsarki. Don haka mun ɗauki matakan gaggawa,” inji shi.
Tinubu ya jaddada cewa dokar ta-ɓaci da aka ayyana kwanan nan kan tsaron ƙasa ba magana ce kawai ta siyasa ba, alama ce ta sabunta niyya wajen ƙara yawan jami’an tsaro, inganta leƙen asiri, da aiwatar da muhimman sauye-sauye ciki har da ƙarfafa yunƙurin kafa ’Yan Sandan Jihohi a matsayin mafita da ta fi dacewa da al’umma wajen magance barazanar cikin gida.
“Sanarwar da aka yi kwanan nan ta ayyana Dokar Ta-ɓaci kan tsaron ƙasa tana nuna irin yadda muke ɗaukar wannan ƙalubale. Ba sanarwa ce ta fatar baki kawai ba; sanarwar yaƙi ce da dukkan nau’o’in rashin tsaro. A wani ɓangare na wannan mataki, mun fara aiwatar da ƙara ƙarfin rundunonin sojoji da jami’an tsaro—ta fuskar yawan ma’aikata, manyan makamai, da ƙwarewar leƙen asiri. Za mu kamo maƙiyan ƙasar mu ko ina suke domin dawo da zaman lafiyar da kowane ɗan Nijeriya yake da haƙƙin morewa.
“Amma domin tabbatar da tsaron jama’a na dindindin, dole mu gyara tsarin tsaron mu tun daga tushe. Shi ya sa gwamnati na take goyon bayan ƙudirin kafa ’Yan Sandan Jihohi. Muna da yaƙinin cewa tsarin tsaro da ya fi kusanci da al’umma zai taimaka wajen cike guraben da rundunonin tarayya ba za su iya cikewa kaɗai ba. Haka kuma zai ƙara samar da ayyukan yi a matakin ƙananan hukumomi. Wannan babban mataki ne, na dole, wanda ya shafi kundin tsarin mulki, kuma mun ƙudiri aniyar ganin an kai ga nasara.”
Shugaban Ƙasa ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na ƙara ƙaimi a mu’amalar diflomasiyya ta ƙasashen duniya domin gyara labaran ƙarya da ke murguɗa kyakkyawar mu’amala da zaman lafiya da ke tsakanin addinai a Najeriya.
Da yake tunawa da gagarumar gudunmawar da marigayi Yarima Abubakar Audu ya bayar, Shugaban ya bayyana shi a matsayin ginshiƙi a tafiyar cigaban dimokiraɗiyyar Najeriya.
Ya ce marigayi Yarima Audu jagora ne mai hangen nesa wanda ya taimaka wajen gina harsashin mulkin Jihar Kogi da kuma sauƙaƙa wa Nijeriya samun kwanciyar hankali a mulkin farar hula.
Ya ce tafiyar siyasar Yarima Audu ba takan burin ƙashin kan sa ba ce, amma gudunmawa ce mai ɗorewa wajen gina ƙasa da ƙarfafa cibiyoyin mulki.
Tinubu ya ce shi ma yana kallon jagoranci daga irin wannan hangen nesa, inda auna aiki yake ta fuskar tasiri, ba yabo ba.
“Mun taru a nan ne domin girmama gwarzo. Mutum wanda sunan sa ya zama ɓangare na tarihin tafiyar mu ta dimokiraɗiyya.
“Yarima Abubakar Audu ba ɗan siyasa kawai ba ne; jagora ne mai haskaka hanya. A matsayin sa na gwamna na farko da aka zaɓa ta dimokiraɗiyya a Jihar Kogi—tun a 1992, sannan kuma a matsayin jagora a 1999—Yarima Audu ya shimfiɗa hangen nesa ga Jihar Kogi tare da taimaka wa a gina harsashin dimokiraɗiyyar ƙasar mu.
“Aboki na ne na ƙut-da-ƙut, ɗan’uwa na a gwagwarmaya, kuma ɗaya daga cikin manyan gwanayen da suka nuna jarumta wajen gina tubalan dimokiraɗiyyar da muke jingina da ita a yau.
“Gadar da ya bari ba tarihi ne kawai ba; misali ne mai rai na jagoranci mai ƙarfi da gwamnati mai sauya al’amura. Wannan misali ne da wannan gwamnati ta ɗauki alwashin girmamawa, ba da baki kaɗai ba, har da aiki.”
Yayin da yake hasashen cigaban da ake yi a manyan fannonin tattalin arziki, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa na sabunta tsarin kiwon dabbobi domin mayar da yankunan da ke da tarihin rikici zuwa cibiyoyin cigaban tattalin arziki da zaman lafiya.
“Muna ƙaddamar da cikakken shiri na sabunta harkar kiwon dabbobi. Wannan ya haɗa da samar da gagarumin tsarin kiwo na zamani, ingantaccen kiwon zamani, da haɗa darajar harkar kiwon dabbobi da tattalin arzikin ƙasa.
“Manufar mu ita ce mu mayar da wannan muhimmin fanni daga tushen rikici zuwa tushen arziki—ta hanyar samar da ayyukan yi, tabbatar da wadatar abinci, da kuma wanzar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin manoma da makiyaya.”
Ta hanyar Shirye-shiryen Jinƙan Jama’a, Shugaban ya ce gwamnati na mayar da ’yan Nijeriya a tsakiya wajen gudanar da gwamnati ta hanyar faɗaɗa tallafin kai-tsaye ga mafi rauni, tallafa wa ƙanana da matsakaitan masana’antu, da ba matasa ƙwarewar da za ta ba su damar yin gogayya a tattalin arzikin duniya.
Haka kuma, ya ce gwamnatin sa na aiwatar da faɗaɗa manyan ayyukan more rayuwa fiye da yadda aka saba—daga gyara hanyoyi da layukan dogo zuwa inganta wutar lantarki.
“Muna gina hanyoyin da za su haɗa kasuwannin mu, su ba da kuzari ga masana’antun mu, kuma su haɗa jama’armu.
“Mai girma Gwamna da mutanen kirki na Jihar Kogi, gadon cigaban da Yarima Audu ya fara a Kogi shi ne abin da muka sha alwashin koyarwa da faɗaɗa shi a faɗin ƙasa.”
