Tinubu yana gina ginshiƙi mai ƙarfi na makomar Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu sun fara samar da ribar dimokiraɗiyya ga ‘yan ƙasa.

Ya faɗi haka ne a safiyar yau yayin tattaunawa da ƙungiyoyin goyon bayan jam’iyya mai mulki, wato APC, a ofishin sa da ke Radio House, Abuja.

Idris ya ce: “Mun cika da dama daga cikin alƙawurran kamfen ɗin mu. An kammala batun lamunin ɗalibai, mun kuma kawo ƙarshen almundahanar tallafin man fetur.

“Jihohin mu suna karɓar ƙarin kuɗi, ‘yancin ƙananan hukumomi ya zama na dindindin, kuma kowane yanki yanzu yana da hukumar cigaban sa.

“Tattalin arziƙin mu ya murmure, ajiyar kuɗin waje na ƙaruwa, hauhawar farashi tana raguwa.

“Mun fara manyan ayyukan raya ƙasa a dukkan sassa na tattalin arziki a shiyyoyin ƙasa guda shida.”

Kan batun sababbin umurnin Shugaba Tinubu game da tsaron ƙasa, Ministan ya jaddada cewa Shugaban Ƙasa ya amince da ɗaukar ƙarin jami’ai a sojoji da ‘yan sanda tare da tallafa wa sababbin rundunonin tsaro da gwamnatocin jihohi suka kafa, yana mai cewa wannan mataki zai zama babban sauyi a yaƙin da Nijeriya ke yi da rashin tsaro.

Ya ce: “Muna fuskantar gaggawar buƙatar kawar da ta’addanci da ‘yan bindiga, mu dawo da zaman lafiya, mu kuma ba ƙasar nan zaman lafiya ga kowa da kowa, ba tare da la’akari da ƙabila ko harshe ko addinin sa ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin mu ya tanada.”

Ministan ya sake tabbatar da ƙudirin Gwamnatin Tarayya na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron ƙasar nan.

A ɓangaren ƙarfafa matasa, Idris ya tabbatar da cewa Tinubu zai ci gaba da kare muradun matasa, ya ƙara da cewa a wannan gwamnati, matasa da ba a taɓa yi ba sun samu muƙamai na jagorantar ma’aikatu da hukumomi.

Idris ya shawarci ƙungiyoyin da su ci gaba da shiga cikin yaɗa shirye-shiryen gwamnati da faɗaɗa haskaka nasarorin ta da tasirin ta.

Ya jaddada cewa wajibi ne a tsaya tsayin daka cikin haɗin kai, tare da bin muradun asali da suka kafa suka APC kuma suka ɗore.

Shugabannin tawagar, Misis Adenike Abubakar da Dakta Abiola Moshood, a madadin ƙungiyoyin, sun sha alwashin ci gaba da bayar da goyon baya ga Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaba Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *