Gwamnatin Tarayya a yau ta yi kyakkyawar tarba ga ‘yan ƙwallon mata, wato Super Falcons, bayan dawowar su daga Rabat, babban birnin ƙasar Morokko, inda suka lashe gasar Kofin Afrika na Mata ta CAF ta shekarar 2024 a matsayin zakarun Afrika.
A cikin wata sanarwa, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana nasarar a matsayin fiye da cin gasar wasanni kawai, yana mai cewa, “nasarar wata shaida ce ta jajircewa, ƙwazo, da ƙarfin gwiwar ‘yan Nijeriya wadda Super Falcons ta nuna.”
Da yake jawabi a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnatin Tarayya, Ministan ya yaba wa ‘yan wasa, da masu horaswa da tawagar ma’aikatan su bisa jajircewar su da sadaukarwar su.
Ya ce: “Kun zamo abin koyi ga matasa a Nijeriya, kuma kun nuna irin tasirin da wasanni suke da shi wajen haɗa kan jama’a da kuma ƙarfafa gwiwa.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu tana da cikakken ƙudiri wajen ci gaba da saka jari a fannin wasanni da tallafa wa ‘yan wasa, ta hanyar samar da ababen more rayuwa da matakan da za su ba su damar yin fice.
Yayin da Super Falcons ke shigowa Abuja, ‘yan Nijeriya sun fito sun tarbi ƙungiyar a lokacin tafiyar da suka yi daga ƙofar birnin Abuja zuwa Dandalin Eagle har zuwa Fadar Shugaban Ƙasa, inda aka karɓe su a hukumance.
“Super Falcons sun ɗaga tutar Nijeriya sama, sun kuma kawo farin ciki ga miliyoyin ‘yan ƙasa. Barkan ku da dawowa, zakarun Afrika!” inji shi.
A ranar Asabar dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Super Falcons ɗin murna kan nasarar da suka samu a gasar.
A takardar sanarwa wadda Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai, Mista Bayo Onanuga, ya rattaba wa hannu, Tinubu ya ce, “Gagarumar nasarar da Super Falcons suka samu a daren yau a Rabat, inda suka zo daga ‘yan sahun baya suka buge Marokko da ke da ƙarfi kuma a gaban ‘yan kallo masu shauƙi, alama ce ta jan halin da ‘yan Nijeriya suke da shi.
“Tare da aiki tukuru, sadaukarwa da jajircewar, kun cimma nasarar da ƙasar nan take fatan samu kuma take addu’a a kai. Ƙasar nan tana sa ran yin kyakkyawar tarba ga gwarzayen mu. Muna murna! Nijeriya tana ɗokin ku.”