Wata Yarinya Ta Zama Mataimakiyar Shugaban Najeriya Ta Rana Daya

Da yake jawabi yayin ganawarsa da tawagar PLAN International karkashin jagorancin Daraktar inganta fasahar kirkire-kirkire ta kungiyar, Helen Mfonobong Idiong a ranar Litinin, Sanata Kashim Shettima ya gayyaci wata matashiya, Joy Ogah, don ta zauna a kan karagar Mataimakin Shugaban Kasa ta yi jawabi ga al’ummar kasa kan kudiri inganta hakkokin ƴaƴa mata

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa mahalarta taron cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sadaukar da kai wajen inganta ilimin ‘ya mace a duk fadin Najeriya.
Shettima ya ce, cikin matakan gwamnati na tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata, akwai babban shirinta mai muhimmanci na ciyar da yara a makarantu a faɗin Najeriya inda milyoyin yara mata ke samin ilmi da abinci kyauta, duba da cewa samar da abinci mai gina jiki ga yara na basu cikakkiyar lafiya da kuzarin da gina ƙasa kamar Najeriya ke matukar bukata.

Shettima ya ce, samin mata masu rajin inganta rayuwar yan uwansu mata irinsu Shuhuda Ahmad, Hauwa Liman, da Rahma Abdulmajid da ma wasunsu a fadar gwamnati, ƴar manuniya ce ga irin yadda Shugaba Tinubu ke baiwa mata masu kishin mata ƴan uwansu muhimmancin da ya dace.

“Za mu ci gaba da tattaunawa da kungiyar PLAN International don ganin inda gwamnati za ta shigo da karfinta wajen aiwatar da shawarwarku kan ƙara inganta ilimin ‘ya mace,” Mataimakin Shugaban Kasa ya ƙara jaddada wa tawagar.

Shettima ya ci gaba da bayyana wa tawagar cewa “in dai Shugaba Bola Tinubu ne, ina tabbatar maku da cewa kun sami abokin aiki na amana wanda za ku iya dogara da shi akan muradunku”

Mataimakin Shugaban Kasa ya kuma bayyana Uwar Gida, Sanata Oluremi Tinubu, a matsayin zakarar gwajin dafi kan yadda macen da ta sami iko da ilmi da kyakkyawan tallafi za ta iya zama babbar jagora inda ya zayyano aiyyukan da uwar gidan Shugaban ta yi a Majalisar Dattawan Najeriya musamman a bangaren muhawara kan manufofin da suka shafi ilimin ‘ya mace.
“Ina so in tabbatar muku, a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, cewa wannan gwamnati tana goyon bayan duka jinsi, mun yi imani da ba za mu nuna wariya ga rabin al’ummarmu sannan mu yi tsammanin za mu sami ci gaba a matsayin kasa ba,” in ji shi.
Mataimakin Shugaban Kasa ya tabbatar wa da PLAN International cewa kofofin gwamnati a buɗe suke don ci gaba da tattaunawa, ya ƙara da cewa, “Matan da ke cikin tawagata su ne mafi dacewa don tattaunawa da ku.”

Bayan jawabin nasa, ita ma Joy Ogah wadda ta karbi kujerar Shettima ta rana daya ta yi nata jawabin daga kan kujerar Mataimakin Shugaban Kasa inda ta nuna godiya kan damar da aka ba ta na wakiltar miliyoyin ‘yan matan Najeriya.

Ogah ta ankarar da cewa, yara miliyan 10.5 a Najeriya ba sa zuwa makaranta, kuma sama da kashi 60 cikin wannan adadin mata ne.
Ogah ta jaddada cewa ‘yan matan Najeriya na iya zama shugabanni idan hukumomin da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki suka aiwatar da matakan da suka dace. Ta yi kira ga gwamnati, da masu ruwa da tsaki, da ma ‘yan kasa da su dauki matakai na bai daya kan inganta ilimin ‘ya mace.

“Dole ne mu saka hannun jari a ilimi da tsaro da kare ƴancin kowane yaro a Najeriya,” in ji ta.

Ogah ta bukaci hukumomin da abin ya shafa da su aiwatar da dokokin da ke kare haƙƙoƙin kowace ‘yarinya mace kuma ta jaddada bukatar samar da kayan tsafta kyautar jiki, musamman audigar mata a makarantu, da kuma tabbatar da samun ruwa mai tsafta, da abinci mai gina jiki ga yaran Najeriya.

“Idan an kare ‘ya’ya mata, zaman lafiya zai zo cikin ruwan sanyi,” ta kara da cewa.
Ta ci gaba da cewa: “duk ni ce Mataimakiyar Shugaban Kasa ta rana daya, amma gwagwarmayar da nake wakilta ba za ta iya karewa a rana daya ba. Za a ci gaba da jin amonsu a cikin manufofinmu, ajujuwanmu, tattaunawarmu, da kuma kasafin kuɗinmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *