Yadda Hukumomin Tsaro Suka Cafke Manyan Shugabannin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ansaru – Ribadu

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun samu babbar nasara da cafke manyan shugabannin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru mai alaƙa da Al-Qaida. Ya ce wani samame da aka gudanar tsakanin watan Mayu da Yuli ya tarwatsa jagorancin ƙungiyar, tare da yin babban lahani ga ayyukan ta’addanci a ƙasar. Ribadu ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce aikin ya samu nasara ne ta haɗin gwiwar rundunar soji, hukumomin leƙen asiri da sauran jami’an tsaro.

Ribadu ya bayyana cewa samamen ya gudana ne a ciki da kewayen Kainji National Park, wanda ya shafi jihohin Neja da Kwara, tare da haɗin kai daga kasashen waje kamar Benin. Ya bayyana sunayen waɗanda aka cafke a matsayin Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar) wanda ya rike matsayin “Amir na Ansaru”, da kuma mataimakinsa Mahmud Al-Nigeri (Malam Mamuda) wanda shi ne shugaban ma’aikata na ƙungiyar. Duka biyun, a cewar Ribadu, sun dade suna cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya.

Ribadu ya ce Abu Bara shi ne wanda ke da alhakin kafa ƙananan ƙungiyoyin barayi a sassan ƙasar, tare da tsara manyan hare-haren garkuwa da mutane da fashi da makami domin samar wa ƙungiyar kuɗaɗe. Shi kuwa Malam Mamuda ya samu horo a Libya tsakanin 2013 zuwa 2015 daga ƙwararrun ‘yan jihadi na ƙasashen Misira, Tunisia da Algeria, inda ya kware wajen sarrafa makamai da kera bama-bamai. A matsayin shugabanni, su ne suka jagoranci hare-haren ta’addanci da dama ciki har da kai farmaki gidan yarin Kuje a 2022, harin wurin ma’adinan Uranium a Neja, garkuwa da injiniyan Faransa Francis Collomp a Katsina a 2013, sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba a 2019 da kuma sace Sarkin Wawa.

Ya ƙara da cewa cafke wadannan manyan shugabannin ya nuna an rushe cibiyar jagorancin Ansaru, kuma hakan na nuni da cewa an shiga sabon mataki wajen kawo ƙarshen rashin gaskiya da tsananin zaluncin shugabannin ta’addanci a Najeriya. Ribadu ya bayyana cewa an kuma gano muhimman bayanai da na’urorin zamani a wajen aikin, wanda ake ci gaba da bincike akansu domin samun karin bayanai kan sauran ƙungiyoyin Ansaru da alaƙarsu da ƙasashen waje. Ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa jagoranci, da kuma rundunar soji da hukumomin tsaro bisa jajircewa, sannan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari wajen murkushe ta’addanci da tsananta tsaro a ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *