Yadda Tinubu Ya Ɗau Saitin Bunƙasa Tattalin Arziki Kan Sahihiyar Turbar Siyasa

Daga Tanimu Yakubu

A jawabin sa ranar bikin cika shekara biyu kan mulki, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, “mun samu gagarimin ci gaba.” Wannan kuwa an gani, kuma an shaida.

A farkon shekarar 2024, darajar Naira ta faɗi warwas sai da N1,800 ta koma daidai da Dalar Amurka $1. Hakan ya jefa magidanta da iyalin su da harkokin kasuwanci cikin ƙaƙa-nika-yi.

Amma yayin da aka kai cikin watan Agusta, 2025, har Naira da farfaɗo, darajar Dala ta koma N1,525. Wannan bai tsaya ga nasarar farfaɗo da darajar Naira kaɗai ba, yana kuma ƙara tabbatar da hujjar yadda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke tafiyar da tattalin arzikin bisa sahihiyar turbar siyasa.

Shugaba Tinubu yana gina nagartaccen tattalin arziki bisa ginshiƙai uku: kuɗin ƙasa masu daraja, nagartattun ayyukan raya ƙasa da kuma bunƙasa ƙarfin makamashi.

Inganta darajar Naira shi ne farkon abin da aka soma. Aka ƙyale Naira ta samar wa kanta daraja da ƙima a kasuwa, aka warware matsalar musayar kuɗaɗen waje ta Dala biliyan huɗu $4. Kuma ana samun maƙudan kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Sannan ‘yan kasuwa suna samun tagomashi. Su kuma ɗalibai masu karatu a waje an rage masu shakku da jimami da ɗarɗar wajen biyan kuɗaɗen karatu. Su kuma masu zuba jari, sun samu yaƙinin cewa gwamnati ta ɗauki nauyin haƙƙin da ke kanta. Nan da nan sai Naira ta tsaya da ƙafafun ta, ta daina faɗuwar-‘yan-bori.

Samar da ayyukan raya ƙasa shi ne ginshiƙi na biyu a tsarin mulkin Tinubu. Ya narka fiye da Naira tiriliyan 5.9 wajen aiwatar da ayyuka daban-daban a Yankin Arewa Maso Yamma, yankin da ya fi tinƙaho da shi wajen samun mafi yawan ƙuri’u. Ayyuka ne kuma waɗanda dukkan sassan ƙasar nan za a ci moriyar su. Sai aikin tagwayen titina na Kaduna zuwa Kano, sai na Kano zuwa Maiduguri, sai babban aikin titin Sokoto zuwa Illela, waɗanda ayyukan titi ne da za su rage wa manoma da ‘yan kasuwa cin dogon zango sannan su samu rage biyan kuɗin zirga-zirga da sufuri.

A matsayin Legas na cibiyar hada-hadar kasuwanci, ta na samun tagomashin gyare-gyare yadda za a samu sauƙin sufurin kayayyaki daga Arewa zuwa tashoshin ruwa ko daga tashoshin ruwan kudu zuwa arewa. Su ma masu masana’antu a Kudu Maso Gabas za su samu sauƙin danganawa kasuwannin Kudu Maso Yamma. Saboda haka gina nagartattun titina a hanyar Legas alheri ne ga ƙasa baki ɗaya, ba wai bajinta ce aka yi wa wani yanki shi kaɗai ba.

Amma kuma idan aka samar da ingantattun titina ba tare da an samar da lantarki ba, to an yi ba a yi ba kenan. Saboda haka da aikin samar da wuta mai ƙarfin kilowat 255 a Tashar Makamashi ta Kaduna, ya nuna irin muhimmancin wutar lantarki ga ayyukan raya ƙasa. Haka su ma masana’antu idan suka samu ƙarin wutar lantarki, za su tsawaita lokutan aiki, ta yadda za su ɗauki ƙarin ma’aikata. Su ma ƙananan asibitoci za su samu dama da sauƙin adana magungunan su a cikin firinji. Ɗalibai za su samu damar karatu a natse cikin hasken lantarki, maimakon su riƙa fama da sayen kananzir suna kunna fitilu.

Shirin Inganta Fannin Noma ta hanyar amfani da sola a Zamfara ya nuna yadda za a iya amfani da makamashi ya amfani gonaki da ɗimbin manoma har ma da masana’antu.

Babban da aka fi ci wa buri shi ne ‘Tinubu National Beltway’, wato manyan titunan da za su yi wa ƙasar nan ‘shan-bante’ da zai tashi tun daga Kalaba sai ya dangana Maiduguri. Daga Maiduguri sai ya dangana har Sokoto. Amma fa ba shi kaɗai su manya-manyan ayyukan da ake magana ba. Ga aikin da ake magana na titin Badagry zuwa Legas, ga titin Illela zuwa Sokoto, ga kuma na Legas zuwa Kalaba. Dukkan su titina ne masu tagwayen hanyoyi da za a shimfiɗa a faɗin ƙasar nan domin inganta tattalin arziki ta hanyar sauƙaƙa sufurin kayayyaki da fasinjoji a tsakanin jihohin arewaci da kudancin Najeriya baki ɗaya.

Wannan aiki da Shugaba Tinubu ya sa a gaba, ci gaban ci gaba ne daga wasu ayyukan gwamnatin da ya gada ta marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya bijiro da wasu ayyukan zirga-zirgar jiragen ƙasa, gadoji da babbar gadar ‘Second Niger Bridge’. Shi kuma Tinubu ya faɗaɗa waɗannan ayyukan raya ƙasa. Hakan ya nuna shugabannin biyu ba su tsaya adawa irin ta gwamnatin da ta shuɗe da wadda ta gaje ta ba. Sai ya kasance wannan gwamnatin ci gaba ta yi da ayyukan da ta gada. Buhari ya aza harsashin gini, shi kuma Tinubu ya ɗora nagartaccen gini bisa ingantattun ginshiƙai, za shi kammala baki ɗaya. Wannan kuwa kyakkyawar haɗakar ci gaban ayyukan raya ƙasa ne a ƙarƙashin sahihiyar dimokraɗiyya.

Masu kushe da adawa na cewa wannan duk farfaganda ce, har suka riƙa watsa wani jadawalin boge, suna ƙarya cewa wai Legas ta fi Arewa baki ɗaya cin moriyar wannan gwamnati. Sai ga shi gaskiya ta bayyana. Direban da a yanzu ya rage yawan sa’o’in da yake ɓatawa kan titi saboda an gyara manyan titinan ya shaida haka. Haka ɗan kasuwar da kayan sa ke isa har Legas a cikin ƙanƙanin lokaci, sun tabbatar da haka. Masu watsa jadawalin ayyukan boge kuwa shiru ka ke ji, wai uwar gulma ta yi cikin-shege.

An daɗe a ƙasar nan ana fama da ayyukan da suka kakare ba a kammala a gwamnatocin baya ba. Ga farashin ayyukan na hauhawa koda yaushe. Ga matsin tattalin arziki da jama’a suka yi fama.

Matsalar tsaro ta riƙa yin barazana ga tituna, yadda tsakar dare titunan ba za su iya biyuwa ba, saboda masu garkuwa da mutane. Haka idan babu nagartaccen tsarin kasuwanci, hada-hadar musayar kuɗaɗen waje za ta fuskanci barazana.

Duk da haka, Tinubu ya yi namijin ƙoƙari a bayyane. Darajar kuɗin ƙasa ya haifar da rige-rigen zaburar da harkokin kasuwanci. Manyan titina sun dunƙule sassan ƙasar nan wuri ɗaya, an samu sauƙin hada-hada. Ƙarin ƙarfin wutar lantarki zai ƙara yawan kayan da masana’antu ke sarrafawa da ƙara wa ƙasa daraja. Sannu a hankali a cikin shekaru biyu Tinubu ya haɓɓaka ayyukan da Buhari ya fara, shi kuma ya shimfiɗa tattalin arziki a faɗin Najeriya bisa, kyakkyawar turbar siyasa.

*Dakta Tanimu Yakubu shi ne Babban-Darakta,
Ofishin Kasafin Kuɗaɗe na Tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *