Za mu biya bashin da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin Gwamnatin Tarayya tun daga 2015 —Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa kamfanonin samar da wutar lantarki (GENCOs) cewa gwamnatin tarayya za ta biya bashin da suke bin ta bayan kammala cikakken bincike da tantance adadin da ake ikirari. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani taro da wakilan kungiyoyin GENCOs a fadar gwamnati da ke Abuja, inda ya ce dole ne a tabbatar da gaskiyar duk wani adadi da za a biya, domin hakan zai zama ginshiki wajen habaka masana’antu da tattalin arziki.

Mai ba Shugaban kasa shawara kan makamashi, Ms Olu Verheijen, ta bayyana cewa gwamnati ta tantance bashin da ya kai naira tiriliyan 4 daga shekarar 2015 zuwa karshen 2023, inda aka riga aka tabbatar da tiriliyan 1.8. Ta ce shugaban kasar ya amince da shirin fitar da takardar biyan bashi na naira tiriliyan 4 domin rage matsin lambar kudin da ke addabar bangaren wutar lantarki, tare da jaddada cewa bashi da aka tantance aka tabbatar ne za kaɗai a biya.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yabawa jagorancin Tinubu, inda ya ce a karkashin mulkinsa an samu nasarori da suka hada da karuwar kudin shiga daga naira tiriliyan 1 a 2023 zuwa tiriliyan 1.7 a 2024, da kuma karin megawatt fiye da 700 ta hanyar shirin PPI.

Manyan ‘yan kasuwa irinsu Tony Elumelu da Kola Adesina sun bukaci gwamnatin ta hanzarta biyan bashin, domin kaucewa rufe masana’antu da durkushewar ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *