Ashafa Murnai Barkiya
A ranar Laraba ce Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya karɓi baƙuncin tawagar Cibiyar Zuba Jari ta Ƙasa da Ƙasa ta Birtaniya, wato ‘British International Investment’ (BII).
Tawagar na ƙarƙashin jagorancin shugaban su, Diana Layfield, kuma sun samu rakiyar Babban Jakadan Birtaniya a Nijeriya, Mista Richard Montgomery. Haɗuwar ta CBN da BII dai wani hoɓɓasa ne domin ƙara ƙarfi da ingancin sauye-sauye da tsare-tsaren kuɗaɗe, domin ƙara jawo ɗimbin masu zuba jari daga waje, kuma a daɗe ana cin moriyar juna.
Gwamna Cardoso ya ƙara jaddada jajircewar da CBN ke yi wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya bisa nagartacciya hanya mai ɗorewa. Sai kuma tafiya ɗoɗar bisa ƙaƙƙarfan tsarin bankuna mai jure ƙalubale.
