Daga Bala Musa Minna
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, wacce ake kira Progressives Governors’ Forum ( PGF ) ta kawo wata ziyara ga gwamnan jihar Neja, Rt. Hon Umaru Muhammed Bago a jiya Litinin domin jajanta wa al’ummar jihar a kan matsalolin ambaliyar ruwan sama tare da rashin tsaro da ke faruwa a fadin jihar da suka janyo hasarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban kungiyar ta PGF kuma gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya jagoranci ziyarar.
Da yake jawabinsa a wajen taron, wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, Sanata Uzodinma ya bayyana cewa, manufar ziyarar da suka yi ita ce, jajanta wa gwamnan Neja Bago tare da al’ummar jihar.
Ya ce ” muhimmin abin da ya dace duk membobin kungiyar su rika yi shi ne, bayyana hadin kan da ke tsakanin ‘ya’yan kungiyar, fiye da abin da ya raba su . Inda ya bayyana cewa, kada su rarraba kan membobi.
Ya ce “mun zo ne wajen abokin aikinmu wato gwamna Bago, da al’ummar jihar a kan matsalolin ambaliyar ruwan sama, rashin tsaro, gobarar wuta da sauransu da ke faruwa a fadin jihar.
Wanda ya ce, ya kamata duk masu ruwa da tsaki su ba da tasu gudummawar da ta dace domin magance faruwar wadannan hadurran a jihar.
Sannan ya yaba wa gwamna Bago a kan ayyukan ci gaban al’umma jihar da yake gudanarwa. Kuma ya nemi al’ummar jihar su bai wa gwamnan goyon baya don samun nasarar bunkasa jihar a fannonin rayuwar al’umma
Haka nan, gwamna Uzodinma ya bayyana cewa, “kungiyar PGF tana goyon bayan tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen karfafa tsaro, samar da muhalli ga al’umma da sauran ayyukan ci gaban mutane,” in ji shi.
Da yake jawabin godiya ga wadannan gwamnonin da suka ziyarci jihar, gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya bayyana cewa, jihar Neja tana fama da matsalolin tsaro, ambaliyar ruwa da hadurran gobara da sauransu. Kuma ya yaba ziyarar da suka kawo gare shi.
Ya bayyana cewa, wannan ya nuna akwai hadin kai tsakanin su da juna a wannan tafiyar da suke yi na goyon bayan manufofin shugaba Tinubu.
Sannan ya yaba wa shugaba Tinubu, hukumomin tsaro, manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da sauransu, domin gudummawar da suke bai wa jihar wajen ci gabanta.
Shi ma Sarkin Bida Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ya yaba wa ziyarar da gwamnonin suka kawo don jajanta wa al’ummar jihar a kan matsalolin da suka faru, wadanda suka janyo hasarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Inda ya bayyana cewa ziyarar za ta karfafa zumunci tsakanin su da juna.
Gwamnonin PGF da suka ziyarci jihar Neja a shekaranjiya Litinin sun hada da Babajide Sanwo-Olu na Lagos, Biodun Oyebanji na Ekiti, Sheriff Oborevwori na Delta, Francis Nwifuru na Ebonyi, tare da Ahmed Usman Ododo of Kogi.
Sai mataimakan gwamnonin jihar Kebbi, Abubakar Umar Argungu; Aminu Usman, na Jigawa; tare da Idris Mohammed Gobir na jihar Sakkwato.
