ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2024

GWAMNA DAUDA LAWAL YA AMINCE ƘARIN ALBASHIN WATA ƊAYA GA MA’AIKATAN ZAMFARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da biyan ƙarin albashin wata ɗaya ga ma’aikatan gwamnatin Jihar. Shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ne ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da aka bayar a ranar 28 ga watan Disamba…

GWAMNA LAWAL YA RATTABA HANNU KAN KASAFIN KUƊIN NAIRA BILIYAN 546 NA SHEKARAR 2025

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira 546,014,575,000.00. Kasafin kuɗin 2025 mai taken; “Kasafin Ceto 2.0”, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara ya gabatar wa gwamnan a ranar Alhamis a gidan gwamnatin…

Zarge-zargen Shugaban Sojin Nijar kan Nijeriya ba su da tushe, cewar Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaryata zargin da Shugaban Sojin ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, inda ya zargi Nijeriya da haɗa kai da Faransa domin tayar da zaune tsaye a ƙasar…

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu a turereniya, ta ba da shawara kan bukukuwan Kirsimeti

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa iyalai da ‘yan’uwan waɗanda suka rasa rayukan su a hatsarin turereniya yayin rabon abinci da aka yi a Ibadan, Abuja, da Okija. A cikin wata sanarwa da…

Ministan Yaɗa Labarai da Darakta Janar na VON sun yi alhinin rasuwar babbar ‘yar jarida Rafat Salami

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa iyalan Hajiya Rafat Salami, babbar ‘yar jarida a gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) kuma Ma’ajin Cibiyar Yaɗa Labarai ta Duniya (IPI), wadda ta rasu a ranar Juma’a…

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba da tsarin Tinubu kan raya albarkatun kiwo da samar da abinci

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan kafa Ma’aikatar Raya Albarkatun Kiwon Dabbobi, ya ce hakan wani muhimmin tsari ne na amfani da damar da ke cikin ɓangaren…

Ministan Yaɗa Labarai ya ƙaddamar da ginin Radio House da aka gyara, tare da alƙawarin ƙarin gyare-gyare

Hoto: Minista Idris yana karɓar kambin karramawa daga Shugabar ƙungiyar ma’aikatan Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Kwamared Chika Ukachukwu a lokacin taron ƙaddamar da gyararren ginin Radio House Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris,…

GWAMNA DAUDA LAWAL YA ƘADDAMAR DA AIKIN HANYA A RIBAS, YA JINJINA WA GWAMNA FUBARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa ƙoƙarin Gwamna Siminalayi Fubara kan ayyukan raya ƙasa daban-daban a Jihar Ribas. Gwamna Lawal ya kasance babban baƙo na musamman a wajen ƙaddamar da aikin titin da gadojin Opobo, wanda ya gudana…

GWAMNA LAWAL YA RABA KUƊAƊE SAMA DA NAIRA BILIYAN 4 NA SHIRIN NG-CARES GA MUTUM 44,000 A ZAMFARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon kuɗaɗe don tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a jihar. Rabon kuɗaɗen wani ɓangare ne na Farfaɗo da Ayyukan Tattalin Arziki da suka durƙushe a sanadiyyar COVID-19 na ‘NG-CARES’, wanda aka gudanar…

GWAMNA DAUDA LAWAL YA RANTSAR DA SABON KWAMISHINA, YA YI GARAMBAWUL A MUƘARRABANSA

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi garambawul a gwamnatinsa, sannan ya rantsar da wani sabon Kwamishina. A Litinin ɗin nan ne Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci zaman majalisar zartarwar jihar, inda a lokacin zaman ya rantsar da wani sabon…