ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2024

Ranar Ma’aikata: Gwamnan Zamfara zai inganta rayuwar ma’aikatan jihar

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa ta inganta rayuwar ma’aikatan jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne wurin gagarumin taron ranar ma’aikata, wanda aka saba gudanarwa a duk faɗin ƙasar nan a kowace ranar ɗaya ga…

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za a iya daukar shekaru 14 kafin a iya kwashe tarin abubuwan da suka rushe a Gaza

Hoto: Wani yanki na zirin Gaza Tsaunin abubuwan da suka rushe mai yawan gaske ciki harda makaman yaki wadanda ba su tarwatse ba da Isra’ila ta bari a mummunan yakin ta a zirin Gaza zai iya daukar kimanin shekaru 14…

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a yi gaggawar dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila

Hoto: Francesca Albanese, mai rahoto ta musamman ta majalisar dinkin duniya a kan halin da hakkin dan Adam ke ciki a yankunan Falasdinawa da aka mamaye Mai rahoto ta musamman ta majalisar dinkin duniya kan halin da hakkin dan Adam…

Ministan Yaɗa Labarai ya kafa kwamitin kare haƙƙoƙin naƙasassu

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ba da umarnin kafa wani kwamiti mai mutum biyar da zai fito da tsarin aiki da Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa domin wayar da kan jama’a game da ‘yanci da…

Dole sai mun sanya fasahar zamani don yaki da matsalar tsaro, cewar Gwamna Lawal ga Majalisar Ɗinkin Duniya

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin yaƙi da matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya. Gwamnan Jihar Zamfara da wasu gwamnonin jihohi sun gana da Amina J. Mohammed,…

Gwamnan Zamfara ya s ce: Mun kawo gagarumin sauyi a harkar tafiyar da gwamnati

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ƙara jaddada cewa gwamnatin sa ta kawo gagarumar gyara a hanyoyin tafiyar da gwamnati don samar da ci gaba mai inganci a jihar. A Litinin ɗin nan ne Gwamnan ya bayyana haka a lokacin…

Sharhi: Shekaru Goma Bayan Sace ‘Yan Matan Chibok: Nijeriya Ba Za ta Ƙara Biyan Kuɗin Fansa Ba

Daga BOLA TINUBU Yau shekaru goma cur tun da aka sace ‘yan mata 276 cikin dare daga makarantar su da ke garin Chibok a yankin arewa-maso-gabashin Nijeriya. Harin na Boko Haram ya girgiza duniya. Daga London har zuwa Washington, masu…

Gwamnan Zamfara ya halarci hawan sallah a Ƙauran Namoda

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya halarci bikin hawan Durbar a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a ranar Lahadin nan. Masarautar Ƙauran Namoda na gudanar da wani gagarumin biki na musamman bayan Sallar Idi, wanda aka fi sani da Hawan Durbar…

Gwamnati za ta sake zuba kuɗin da ake tarawa daga janye tallafin wutar lantarki wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sama da naira tiriliyan 1 da za a tara daga janye tallafin wutar lantarki za a sake zuba su ne wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi…

Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar kawo ƙarshen ‘yan ta’adda a Zamfara

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga da ta addabi Jihar Zamfara. Shugaban ya kuma bayar da umarnin tura ƙarin sojoji tare da ci gaba da kai farmaki kan ’yan ta’adda…