Gwamnatin Zamfara ta ce ba ta ciwo bashin naira biliyan 14.26 ba
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta ciwo bashin kuɗi Naira Biliyan 14.26 ba, sai dai wani ɓangare na bashin Naira Biliyan 20 wanda gwamnatin da ta shuɗe ta ciwo. A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan…
NAMADI BAI ƊAUKI RAINI BA: Gwamnan Jigawa ya yi hajijiya da jami’an da suka yi wuji-wuji da kuɗaɗe a Manyan Makarantun Koyon Ayyukan Lafiya
A taron Majalisar Zartaswa ta Jihar Jigawa na ranar Litinin, 25 ga Maris, 2024, an amince da ƙudurori kamar haka: Majalisar Zartaswa ta duba Rahoton Kwamitin Tantance Rahoton Kwamitin Bincike a kan Manyan Makarantun Koyar da Ayyukan Kiwon Lafiya na…
Gwamnan Zamfara ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kammala madatsun ruwan jihar
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen ɗaukar nauyi tare da kammala ayyukan madatsun ruwa da ake yi a jihar. Gwamnan ya yi kira a ranar Talata yayin ziyarar aiki da ya kai…
TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA: Kano za ta raba ƙaramin buhun shinkafa lodin mota 100, buhun dawa lodin mota 44, buhun gero lodin mota 14, buhun masara lodin 41 a faɗin jihar
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta yi rabon tallafin kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta ba jihar. Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi wa taron manema labarai a ranar yammacin…
Dole ne mu daina barin bambancin addini da ƙabilanci yana raba kan mu a matsayin mu na ‘yan ƙasa, inji Ministan Yaɗa Labarai
Wata tabbatacciyar hanya ta samun haɗin kan ‘yan Nijeriya wadda ba ta bari bambancin ƙabilanci, addini, da siyasa ya raba kan mu ba ita ce ta samar da wani labari mai ban sha’awa na ƙasa, mai ƙarfafa amana da amincewa…
Matsalar Tsaro: Gwamna Dauda Lawal ya gana da Tinubu
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin tattaunawa kan yadda ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga da matsalolin tsaro a jihar. An gudanar da ganawar ne a ranar Talata cikin sirri a ofishin shugaban…
Gwamnan Zamfara ya nemi a ƙara yawan sojoji masu yaki da ‘yan ta’adda a jiharsa
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi kira da a ƙara yawan sojojin da za a tura Jihar. A ranar Litinin ɗin nan ne Gwamnan ya ziyarci Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, a Hedikwatar tsaro da ke…
Tsaro: Gumi bai fi ƙarfin doka ba, an riga an yi masa tambayoyi, inji Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tuni jami’an tsaro suka yi wa fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, tambayoyi kan kalamansa na baya-bayan nan kan ‘yan bindiga a Nijeriya. Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi…
Ku cusa ɗabi’u nagari a zukatan ‘ya’yan ku, kiran Ministan Yaɗa Labarai ga iyaye
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su jajirce wajen ganin sun cusa halaye masu kyau a zukatan ‘ya’yan su. A wata sanarwa da Mataimaki na…
Kisan ‘yan’uwa 4 a Muzaharar Ashura a Sakkwato:
Kotu ta umarci ‘yan sanda su biya diyyar Naira miliyan 80 Daga Wakilinmu Kotun daukaka kara ta Tarayya da ke zamanta a Sakkwato ta umurci rundunar ’yan sandan Nijeriya su biya diyyar Naira miliyan 80 ga iyalan wasu ’yan’uwa Musulmi…










