ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Month: April 2025

DA DUMI-DUMI! Za a Bai Wa Maniyyatan Najeriya Guzirinsu A Tsabar Kuɗi

A wani yunkuri na tabbatar da cewa ba a sami wata tangarda a aikin Hajjin bana ba,Babban bankin Najeriya ya amince da bai wa hukumar aikin Hajji ta Kasa tsurar kudaden guzirin Alhazai don a raba musu a hannu. Wannan…

UNDP TA YABA WA GWAMNA LAWAL, TA CE GWAMNATIN ZAMFARA TA ZAMA ABIN KOYI GA SAURAN JIHOHI WAJEN TALLAFA WA AL’UMMA

Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa jajircewarsa wajen ba da tallafin da zai amfani al’ummar jihar Zamfara. A ranar Laraba ne hukumar UNDP ta ƙaddamar da Cibiyar Magance Ƙalubalen Ci Gaba…

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Karyata Jita-Jitar Hana Shettima Shiga Villa

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta jita-jitar da ke cewa an hana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shiga fadar shugaban ƙasa. A wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin watsa labarai a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha,…

GWAMNATIN TARAYYA TA SAKI NAIRA BILIYAN 50 DOMIN KYAUTATA WALWALAR MA’AIKATAN JAMI’O’I – MINISTAN ILIMI

Ministan Ilimi na Najeriya, Dakta Maruf Olatunji Alausa, ya sanar da sakin kudade har Naira biliyan 50 da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da su domin biyan hakkokin ma’aikatan jami’o’in tarayya. Wannan mataki yana daga cikin cikar…

Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce nasarar tashin jirgin kasuwanci na farko daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu da ke Minna alama ce ta haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin Gwamnatin Tarayya da…

Ministan Labarai Zai Horas da Ƴan Jaridun Soshiyal Midiya Kan Hanyoyin Watsa Labarai na Zamani

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ma’aikatarsa za ta fara horar da ‘yan jaridun soshiyal midiya kan sabbin hanyoyin yaɗa labarai da kuma amfani da fasahar zamani. Ministan ya bayyana haka ne…

Minista Ya Sake Jaddada Ƙudirin Sabunta Kayan Aikin Watsa Labarai Na Gwamnati

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta sabuntawa da kuma inganta dukkanin kayan aikin watsa labarai na gwamnati, a wani ɓangare na ƙoƙarin ta na gyara fagen yaɗa labarai a…

Na Karɓi Mulki Lokacin Da Jihar Zamfara Ke Fama Da Matsaloli Ta Kowace Fuska– Gwamna Lawal

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana cewa, lokacin da ya karɓi mulki daga tsohon gwamna Bello Matawalle, jihar Zamfara tana cikin matsaloli ta kowace fuska. Ya bayyana cewa rashin tsaro ya yi katutu, tsarin ilimi…

ƘUNGIYAR KASUWANCI TA NIJERIYA DA AMURKA TA KARRAMA GWAMNA LAWAL BISA AYYUKAN INGANTA RAYUWAR AL’UMMA A ZAMFARA

Ƙungiyar Kasuwanci ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal da babbar lambar yabo ta jagoranci da hidimar al’umma. A ranar Asabar ne ƙungiyar ta yi bikin cika shekaru 65 da kafuwa, tare da ƙaddamar da…

Ministan Yaɗa Labarai Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Ilimin Kafofin Watsa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa jami’an gwamnati da ba su da ilimi kan kafofin watsa labarai suna cikin haɗarin faɗawa tarkon yarda da labaran ƙarya. Mataimaki na musamman ga Ministan kan…