ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Month: October 2025

Tinubu ya umarci sabbin hafsoshin tsaro su zama masu hazaƙa wajen yaƙar ta’addanci da barazanar tsaro

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da ya nada su kasance masu samar da sabbin dabaru da jajircewa wajen tinkarar ta’addanci da barazanar tsaro da ke addabar kasar. Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da…

SABUNTA BIRANE: An Samu Ragin Haɗurra a Zamfara Cikin Shekara Guda – FRSC

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa adadin haɗurran mota a jihar Zamfara ya ragu da kashi 6 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024, sakamakon aiwatar da sabbin manufofin tsare-tsare da sabunta birane a jihar. Kwamandan…

Hukumar NELFUND ta raba fiye da Naira biliyan 116 ga ɗalibai sama da dubu 600 tun bayan ƙaddamar da shirin lamunin a Najeriya

Hukumar bayar da lamunin karatu ta Najeriya (NELFUND) ta ce ta raba sama da Naira Biliyan 116.4 ga dalibai fiye da 624,000 tun bayan kaddamar da shirin lamunin karatu a ranar 24 ga Mayu, 2024. A cewar rahoton da hukumar…

An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sanƙarau A Zamfara

A Zamfara, hukumomin kula da yaƙi da cutar shan-inna sun bayyana cewa an yi wa yara fiye da miliyan biyu rigakafin cututtukan mashaƙo da sankaran yara a faɗin jihar, yayin da sama da miliyan 1.8 na yara ‘yan ƙasa da…

Hukumar da ke kula da ayyukan Hukumar Tsaron Ƙasa ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci rubuta jarabawar na’ura mai ƙwaƙwalwa (CBT)

Hukumar da ke kula da ayyukan Hukumar Tsaron Ƙasa, Hukumar Gidan Gyaran Hali, Hukumar Kashe Gobara, da Hukumar Shige da Fice (CDCFIB) ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci rubuta jarabawar na’ura mai ƙwaƙwalwa (CBT) domin daukar sabbin ma’aikata…

Farashin abinci na ƙara sauƙi a Najeriya yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki

Rahotanni daga jihohin Arewa maso Yamma na nuna cewa farashin kayan abinci ya fara raguwa a kasuwanni sakamakon girbin damina mai albarka da manoma suka samu a bana. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba…

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gargaɗi shugabanni da hukumomin tsaro da su guji tattaunawa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai idan har za a bar su da makaman nasu, yana mai cewa irin wannan salon sulhu ba ya kawo…

Ba a tauye ’yancin addini a Nijeriya, inji Ministan Yaɗa Labarai a hirar CNN

.Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ƙara maida hankali wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan domin tabbatar da tsaro da walwalar ’yan ƙasa. Da yake magana…

Gwamnatin Zamfara Ta Warware Matsalar Ɗaliban Ta Da Aka Bari A Indiya

Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Zamfara (ZSSB) ta bayyana cewa Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, ya amince da biyan bashin kuɗin karatun ɗaliban jihar da suka yi karatu a Jami’ar Sharda da ke ƙasar Indiya. Wannan mataki, a cewar hukumar, ya…

Gwamnati ta fara shirin tabbatar da ƙananan manoma sun amfana da sabbin taraktocin Belarus

Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki kan tsare-tsare na musamman domin tabbatar da cewa sabbin taraktocin Belarus da aka ajiye za su amfanar da kananan manoma a faɗin ƙasar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban ƙasa…