ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Month: November 2025

Gwamna Lawal Ya Tabbatar Da Cikakken Goyon Bayan Gwamnatin Sa Ga Jami’ar Kimiyyar Likitanci Da Ke Tsafe

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da bai wa sabuwar Jami’ar Kimiyyar Likitanci da Fasahar Lafiya ta Tarayya da ke Tsafe cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar kafuwarta da ci gabanta. A ranar Litinin…

Gwamnati Ta Roƙi ‘Yan Nijeriya Su Kwantar da Hankali Kan Rikicin Diflomasiyya da Amurka

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su dangane da rikicin diflomasiyya da ake ciki tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi wannan kiran a…

Shugaba Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar…

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana na shekarar 2026

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da rage kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026 ga mahajjata daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu sauƙin kuɗi idan aka kwatanta da na bara. A cikin sanarwar da hukumar ta fitar,…

Gwamnatin Tarayya ta ce farashin kayan abinci ya sauka ne sakamakon manufofin ƙarfafa kasuwa da nufin farfaɗo da noma

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa raguwar farashin kayan abinci da ake gani a kasuwanni a ‘yan kwanakin nan, na da nasaba da manufofi da matakan musamman da aka dauka domin gyara harkar kasuwa da karfafa samar da abinci a cikin…

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta gargaɗi Amurka kan tsoma baki cikin lamurran Najeriya tare da kira ga tattaunawar Diflomasiyya

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana goyon bayanta ga cikakken ikon Najeriya kan harkokinta na cikin gida tare da tabbatar da ’yancin addini da bin doka da oda a kasar. A wata sanarwa da Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) ta fitar,…

Tinubu: Gwamnatin Najeriya Na Ci Gaba da Tattaunawa da Ƙasashen Duniya Ta Hanyar Diflomasiyya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na kan hanyar ci gaba da tabbatar da alaƙar diflomasiyya, yayin da manufofin tattalin arziƙin gwamnati ke fara haifar da sakamako mai gamsarwa a gida da kuma ƙasashen waje. Shugaban ƙasar…

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu -Gwamna Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa samun lambar yabo ta “Gwamna Mafi Nagarta Na Shekara” daga jaridar LEADERSHIP babban ƙarfafawa ce gare shi domin ci gaba da gudanar da ayyuka masu tasiri ga al’ummar jihar. Gwamnan ya bayyana…

Yadda CBN Ke Tallabe Da Tattalin Arzikin Nijeriya, Yayin Da Farashin Ɗanyen Mai Ke Faɗuwar-‘yan-bori A Kasuwa

Daga Ashafa Murnai Barkiya Yayin da farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a duniya, yanzu haka ganga ɗaya ta ɗanyen mai kaɗan ta haura Dala 64. Haka kuwa ga ƙasar da tattalin arzikin ta ya dogara ga kuɗin fetur kamar Nijeriya,…

Jimamin Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa

Daga Tanimu Yakubu Rasuwar Janar Abdullahi Mohammed, GCFR, fss, psc, mni, mni ta kawo ƙarshen wani muhimmin tarihin sadaukarwa ga aikin gwamnati da kuma fannin tsaron ƙasa. Marigayi Janar Abdullahi gwarzo ne da ya nuna tsantsar kishi, sadaukarwa, ɗa’a da…