ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC na nuna raunin jam’iyyun adawa — Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce yawaitar sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC na bayyana raunin da ke cikin jam’iyyun adawa, yayin da APC ke ƙara ƙarfi. Shettima ya bayyana haka ne a Enugu, inda ya wakilci…

Minista Ya Taya Ɗanlami Nmodu Murnar Zama Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Onlayin

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Alhaji Ɗanlami Nmodu murna kan zaɓen sa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Mawallafan Jaridun Yanar Gizo (GOCOP) a zaɓen da aka gudanar a Legas. Idris ya ce: “Malam Nmodu,…

MAGANCE BALA’O’I: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar da aniyar gwamnatin sa ta ci gaba da haɗa kai da Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) wajen inganta tsarin daƙile bala’o’i da haɗurra a faɗin jihar. A wata sanarwa da mai…

Shirin Shugaba Tinubu na rangwamen kuɗin wanke ƙoda ya amfanar marasa lafiya da dama a Jihar Kano

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin rage kuɗin wanke koda daga ₦50,000 zuwa ₦12,000, ragin da ya kai sama da kashi 76 cikin ɗari. Wannan mataki na daga cikin manufofin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu domin sauƙaƙa wa…

NELFUND ta sake buɗe damar tantance ɗalibai don samun Lamuni na shekarar karatu ta 2024/2025

Hukumar Lamunin Ilimi ta Najeriya (NELFUND) ta amince da sake buɗe rukunin tantance ɗalibai karo na ƙarshe har na tsawon awanni 48, domin jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi ba su kammala tantance dalibai masu nema ba. Wannan zai fara ne…

Shugaba Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo murna bisa naɗin sa a matsayin Sardaunan Zazzau

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Namadi Sambo, murna bisa nadin sa da aka yi a matsayin Sardaunan Zazzau daga Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli. Nadin ya gudana ne a ranar Asabar, 11 ga…

NAZARI: Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal

Tun bayan da Gwamna Dauda Lawal ya karɓi ragamar mulkin jijar Zamfara a watan Mayun 2023, jihar ta fara fuskantar wani sabon salo na shugabanci wanda ya shafi kusan dukkan fannoni na rayuwa — daga tsaro zuwa tattalin arziki, daga…

Dalilan da Suka Haifar da Jan-ƙafa Wajen Aiwatar da Ayyukan Kasafin 2024 da na 2025 -Yakubu

Ashafa Murnai Barkiya Babban Darakta a Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya, Tanimu Yakubu, ya bayyana wa Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Darattawa dalilan da suka haifar da samun Jan-ƙafa wajen kammala aiwatar da ayyukan kasafin kuɗaɗe na shekarar 2024 da na 2025….

Yaushe Isra’ila Za TA Sake Bude Yaki Da Iran?

Daga Mujtaba Adam Da aka yi wa wani jami’in gwamnatin Iran tambaya a kan yiwuwar sake buɗe yaƙi a tsakanin Isra’ila da Iran, sai ya bayar da jawabin cewa:“ To dama wa ya ce an kawo ƙarshen yaƙin? Abin da…

Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Na Jagorantar Taron Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a Abuja

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar zaman Majalisar ‘Yan Sanda ta Ƙasa a zauren majalisar da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja. Zaman ya fara ne da ƙarfe 2:39 na rana a yau Alhamis, jim kaɗan bayan Shugaban Ƙasa ya…