ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

An kai mutum 20 da fashewar tankar mai a Suleja ta rutsa da su manyan asibitoci don samun kulawa ta musamman

A bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, an kai waɗanda suka jikkata a haɗarin fashewar tankar man fetur a Suleja zuwa manyan asibitoci don su samu kulawa ta musamman. A cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman kan…

Gwamnatin Tarayya ta umarci tura waɗanda hatsarin tankar mai ya shafa a Suleja zuwa manyan asibitoci

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gaggawa na tura mutanen da suka jikkata a hatsarin fashewar tankar man fetur da ya faru a Suleja, Jihar Neja, daga Asibitin Suleja zuwa manyan asibitoci domin samun ingantacciyar kulawar lafiya cikin sauri. Ministan…

Nijeriya na da ‘yan kurkuku sama da 48,000 da ke jiran yanke hukunci – NCoS

Daga Abubakar Musa Sama da ‘yan kurkuku 48,000 a Nijeriya masu jira a yanke masu hukunci ne (ATPs), kamar yadda Sylvester Nwakuche, mai rikon kwarya a hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya (NCoS) ya bayyana. Kamar yadda kafar…

Gwamnatin Isra’ila ta amince da tsagaita wuta da Hamas

Daga Abubakar Musa Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma matsayar musayar fursunoni da Hamas a awowin farko na safiyar ranar Asabar, wanda hakan ke nuni da cire wani shamaki domin samar da sauki ga zirin Gaza…

Tinubu ya himmatu wajen kammala hanyar Abuja zuwa Kano cikin watanni 14, cewar Ministan Yaɗa Labarai

Hoto; Alhaji Mohammed Idris tare da Ministan Ayyuka Dave Umahi da sauran jami’ai a garin Tafa Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da jajircewar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi na kammala…

Ba mu buƙatar amincewar Sanusi kan tsare-tsaren mu na tattalin arziki, inji Ministan Yaɗa Labarai

Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan kalaman Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan tsare-tsaren gyaran tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take aiwatarwa, tana mai bayyana su a matsayin marasa amfani kuma na son rai. A wata…

Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai kan nasarori, ta nemi ƙarin kasafin kuɗi na musamman ga ma’aikatar

Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, bisa ƙoƙarin sa wajen gudanarwa da yaɗa bayanai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati. An yi masa wannan yabon ne a ranar Talata yayin da ya…