ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Dantsoho Ya Nemi Ƙasashen Afrika Su Hada Kai Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwan Yankin

Daga Bello Hamza, Abuja Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) kuma Shugaban Ƙungiyar Gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Yamma da Tsakiyar Afirka (PMAWCA), Dr. Abubakar Dantsoho, ya yi kira ga ƙasashe mambobinsu da su ƙarfafa…

Gwamnatin Tinubu ta mayar da martani kan matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ’yancin addini

Gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake ganin suna take ’yancin yin addini. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris…

China ta bayyana goyon baya ga Najeriya tare da gargaɗin tsoma bakin ƙasashen waje kan zargin tauye ‘yancin addini

Gwamnatin China ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Najeriya a yayin da ake samun zazzafar muhawara bayan suka daga Amurka kan yadda gwamnatin Najeriya ke tafiyar da batutuwan addini a cikin ƙasa. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta…

Yaudarar Trump Wajen Amfani da Najeriya Don Ceto Makomar Siyasar Sa a Amurka

Rubutawa: Aliyu Samba Akwai wata tsohuwar ka’ida a ilimin siyasa da ake kira “Diversionary Theory of War”, wadda ke bayyana cewa wasu gwamnatoci na iya shiga cikin rikicin wasu ƙasashe ko ƙirƙirar barazana daga waje don karkatar da hankalin jama’a…

Rundunar Sojin Najeriya sun fatattaki gungun ‘yan bindiga a Shanono tare da kashe 19 daga cikin su

Sojojin rundunar hadin gwiwa ta Operation MESA a Jihar Kano sun yi nasarar dakile wani yunkurin hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Shanono, a yammacin ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025. A cewar sanarwar da rundunar ta…

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara na Naira Biliyan 140

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa tana gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa da darajarsu ta kai kusan Naira Biliyan 140 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar, a wani shiri da aka bayyana a matsayin sabon babi na farfaɗowa…

HIKIMAR SHIGO DA ABINCI DAGA WAJE: Yadda Tinubu ya magance tsadar abinci, ba tare da samun cikas ga Shirin Farfaɗo da Noma a Nijeriya ba

Daga Tanimu Yakubu Jaridar Daily Trust ta ranar 6 ga Oktoba 2025, tana ɗauke da ra’ayin ta mai nuni da cewa “Shirin Shigo da Abinci da Gwamnatin Tinubu ke yi yana Gurgunta Harkokin Noma a Arewa.” Ra’ayin jaridar ya nuna…

SHIRIN ƘARFAFA JARIN BANKUNA: CBN ya shawarci bankunan da ba su da ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

Ashafa Murnai Barkiya Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi magana dangane da ƙoƙarin da bankuna ke yi domin ganin sun cika sharuɗɗan adadin ƙarfin jari da CBN ya gindaya masu. Ya ce da yin hakan zai sa…

CBN YA YUNƘURO: Naira ta hana Dalar Amurka numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

Ashafa Murnai Naira ta ci kasuwar ƙarshen watan Oktoba tare da samun galabar Naira 15.33 kan Dalar Amurka, a ranar 31 ga Oktoba. Naira ta samu wannan tagomashin na Naira 15.33 a ranar Juma’a kan Dala a kasuwar ‘yan canji…

CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai Dala biliyan 1.259, domin su shigo da fetur daga waje

Ashafa Murnai Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata wani bauɗaɗɗen rahoton da aka ce ya sayar wa manyan dillalan mai har Dalar Amurka biliyan 1.259, domin su shigo da fetur da dangogin sa daga waje. Cikin wata sanarwar da Kakakin…