ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Year: 2025

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauye a manyan mukaman rundunonin tsaron ƙasar, a wani yunkuri na ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya. A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya fitar…

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 a Borno da Yobe

Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 50 tare da dakile hare-hare da dama da aka kai kan sansanonin sojoji a jihohin Borno da Yobe. Rundunar sojin ta ce ‘yan ta’addan…

Gwamnatin Tarayya ta fara horas da matasa 260,000 a fannoni daban-daban na sana’o’in dogaro da kai

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani shirin horas da fiye da matasa 260,000 a fannonin sana’o’in dogaro da kai a fadin kasar nan, karkashin shirin Technical and Vocational Education and Training (TVET). Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana…

NELFUND ta buɗe tsarin neman lamunin ɗalibai na shekarar karatu ta 2025/2026

Hukumar Lamunin Ilimi ta Najeriya (NELFUND) ta sanar da buɗe shafin yanar gizo na neman lamunin dalibai na shekarar karatu ta 2025/2026, domin bai wa dalibai a fadin ƙasar damar samun tallafin kuɗi don ci gaba da karatu. Manajan Daraktan…

Shugaba Tinubu ya amince da tallafin Naira 250,000 ga ƙananan ’yan kasuwa a Jihar Katsina

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin Naira 250,000 ga ƙananan ƴan kasuwa da matsakaitan masana’antu (MSME) da suka nuna bajinta a yayin Faɗaɗɗen Taron Kanana da Matsakaitan Masana’antu na Ƙasa (Expanded National MSME Clinic) da…

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar da Majalisar Habaka Abinci Mai Gina Jiki Ta Zamfara, Ya Ce Tamuwa Barazana Ce Ga Tattalin Arziki

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa matsalar rashin abinci mai gina jiki ba batun lafiya kaɗai ba ce, illa ce ta tattalin arziki da ke gurgunta ci gaban xan adam. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da…

Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na Goma Na Aikin Jinya Kyauta, An Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala zagaye na goma na shirinta na musamman na aikin jinya kyauta, inda aka kula da marasa lafiya 3,447 daga sassa daban-daban na jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna,…

Wata Yarinya Ta Zama Mataimakiyar Shugaban Najeriya Ta Rana Daya

Da yake jawabi yayin ganawarsa da tawagar PLAN International karkashin jagorancin Daraktar inganta fasahar kirkire-kirkire ta kungiyar, Helen Mfonobong Idiong a ranar Litinin, Sanata Kashim Shettima ya gayyaci wata matashiya, Joy Ogah, don ta zauna a kan karagar Mataimakin Shugaban…

Shugaba Tinubu Ya Taya Sanata Kwankwaso Murnar Zagayowar Ranar Haihuwa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan jahar Kano, kuma shahararren ɗan siyasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau, 21 ga Oktoba, 2025. Shugaban ya taya ƴan uwa da abokan arzikin Kwankwaso da ma…

Gwamnatin Tarayya Na So A Riƙa Amfani Da Hulɗa da Jama’a Wajen Ƙaryata Cewa Ana Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi A Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masana harkokin sadarwa da su yi amfani da fayyace gaskiya tare da kafa hujjoji wajen ƙaryata iƙirarin da wasu ke yaɗawa cewa wai ana yi wa…