Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da sabbin cibiyoyi guda uku na zamani domin kula da masu fama da cutar daji (cancer) a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Cibiyoyin sun haɗa da na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) a jihar Edo, Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya (UNTH) da ke Enugu.
Ministan Yada Labarai na Ƙasa, ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce wannan ci gaba wani ɓangare ne na shirin farfaɗo da harkar lafiya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a fadin ƙasa.
A cewar Ministan, shi da sauran abokan aikinsa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kudi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin kaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a jihar Katsina.
Cibiyoyin da aka kaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sabbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan asibitocin koyarwa na Tarayya a ƙasar.
Wannan ci gaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alkawarin samar da ingantaccen tsarin lafiya ga kowa da kowa a Najeriya.