Abin da ya sa muka buɗe shafin fallasa mazlumiyar Shaikh Zakzaky, In ji Edita Karrar Ashamariy Iraƙi


Karrar Ashamariy, ɗaya ne daga fitattun ‘yan jarida na ƙasar Iraƙi. Shi ne babban Editan Mujallar “Hafeez” ta Alkur’ani da haramin Imamu Husaini (as) yake bugawa. Shi ne mai kula da shafin (Account) @Nijeria-313 da ke manhajar X. Jaridar Almizan ta yi hira da shi a kan dalilin samar da shafin, da yadda ya zamanto muryar yaɗa mazlumiyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) da raunanan Duniya. Wakilinmu Yusuf Kabir ne ya fassara, ya rubuta. Ga dai hirar kamar yadda take:


ALMIZAN: Me ya sa ka samar da wannan dandali na tallata Mazlumiyyar Shaikh Ibraheem Zakzaky?


KARRAR: A lokacin da danniya take ƙaruwa, cin zarafin ƙungiyoyi da fahimtocin addini a wasu ƙasashen duniya yake ƙara yawaita, sai na samar da wannan ‘account’ ɗin (shafin) na yaɗa labarai a dandalin X (wanda ake kira Twitter a da) mai suna “@Najiria_313”. Shafin ya fito fili ya zama dandali na intanet, wanda ke rubutu ta hanyar sauti da hotuna kan zaluncin da ake wa ‘Yan Shi’a na Najeriya. Kuma yana fallasa zaluncin ta hanyar yaɗa hotuna da kalmomi masu isar da saƙon irin girman tsarin danniya da ake yi musu.


ALMIZAN: Yaya ka fara tunanin kafa shafin na @Najiria_313?


KARRAR: Tunanin ya fara ne a shekara ta 2016 bayan mun lura da irin girman zalunci da cin zarafin da ake wa Harkar Musulunci a Nijeriya da jagoranta Shaikh Zakzaky. Haka kafafen yaɗa labaran maƙiya suna suranta kamar ita Hukumar Nijeriya ba ta da laifi a kan kisan kiyashin da ta aiwatar. Duk da girman bala’in da ya faru, ga kuma ƙarancin sanin abubuwan da suka faru, sai muka samar da ‘account’ ɗin domin fallasa laifuffukan da hukumar Nijeriya ta yi, ta hanyar yaɗa hotuna da rahotanni ingantattu. Daga nan ne aka samu tunanin kafa kafar a matsayin hanyar yaɗa haƙiƙanin abubuwan da suka faru.


ALMIZAN: Zuwa yanzu nawa ne adadin waɗanda ke bibiyar ku?


KARRAR: Waɗanda ke bibiyar mu zuwa yanzu sun kai 21,770 daga ƙasashen duniya daban-daban. Mutanen sun haɗa da ‘yan jarida, jaruman nishaɗi, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, Malaman Jami’a da dalibansu, Malaman addini da mutanen da suke damuwa da abin da yake faruwa a nahiyar Afrika. Amma mutanen Iraƙi, Iran, Nijeriya, Misra, Tunusiya sun fi yawa, duk da akwai masu bibiya daga ƙasashen Turawa.


ALMIZAN: Mene ne babbar manufar wannan shafin?


KARRAR: Manufarmu ta asali ta ‘yan’adamtaka ce, kuma ta yaɗa labarai a lokaci guda. Ba mu yaɗa tashin hankali ko tayar da tarzoma, ko tsokana ko wani abu makamancin haka. Muna kawai nuna gaskiyar abubuwan da suka faru ne ya ta hanyar hujjoji na yankan shakka. Bugu da ƙari muna neman samun goyon bayan Hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam da na duniya ga wannan batu da ake yi wa rikon sakainar kashi bisa tsari, a kan a yankewa waɗanda suka aiwatar da hakan hukunci. Haka kuma, muna ƙoƙarin tabbatar da tarihin kafafen dandalin sada zumunta (Social Media) wanda zai rubuta wa ƙarni na gaba abin da ya faru, domin asusun ya zama tushe na ƙasa da na ɗan Adam ga masu sha’awar batutuwan ’yancin addini da kare haƙƙin ɗan Adam a Afirka.


ALMIZAN: Waɗanne mutane ne ke gudanar da shafn tare da ku?


KARRAR: Shafin ana gudanar da shi ne ta hannuna da kaina, tare da haɗin gwiwar ƙwararrun ƙungiyar masana harkar yaɗa labarai. Ba za mu iya bayyana sunayensu ba saboda dalilai na tsaro. Amma ana iya cewa ƙungiyar ta ƙunshi mutane daga Iraƙi, Iran, Lebanon, Najeriya, Tunisiya, da Masar. Kowannen su yana ba da gudummawa daga wurin sa, ko dai ta hanyar fassara, sa ido a fili, gyara labarai, ko kuma fallasa abin da yake faruwa a yau da kullum.


ALMIZAN: Waɗanne manyan ayyuka kuka yi daga samar da shafin?


KARRAR: Mun gabatar da ayyuka da daman gaske, amma ga tsakure daga muhimman abubuwan da muke rubutawa da yaɗawa:-
Kisan kiyashi na Zariya a 2015, inda sojojin Najeriya suka kashe fiye da mutane 348 (wannan bisa lissafin da Sakataren Gwamnatin Kaduna a lokacin Nasiru Ahmad Elrufa’i ya bayyana a gaban kwamitin JCI na Lawal Garba a 2016) daga cikin magoya bayan ƙungiyar Musulunci, kuma aka binne su a cikin ƙabari na bai-ɗaya.
Sai shari’ar kama Shaikh Ibraheem Zakzaky, da kuma fallasa yanayin da yake ciki a gidan yari da kuma yanayin lafiyarsa da irin zaluncin da aka yi masa a sad da yana tsare.
Sai kuma yaƙin wayar da kan al’umma a kan abin da ya faru, don wayar da kai tare da fallasa take haƙƙin aiwatar addini.
Duk wannan na gudana ne ta hanyar zane-zane da wallafe-wallafen a shafukan Intanet tare da fassara abin da ya faru daga Turanci da Hausa zuwa Larabci don yaɗa wa al’ummar Musulmi a duniya.


ALMIZAN: Mene ne burinku na gaba game da wannan shafin naku?


KARRAR: Burinmu ba shi da iyaka game da wannan shafin. Ina fatan yi masa rijista a hukumance, domin yin hakan zai ba shi inganci mafi girma, kuma zai ba mu damar amfani da shi a fannonin ilimi, watsa labarai, har ma da shari’a. Idan asusun ya tabbata, za a yi la’akari da shi a matsayin wata cibiya da aka amince da ita, wanda zai sauƙaƙe mana yaɗa zaluncin Shi’a na Najeriya a duniya, da kuma shiga cikin tarurruka na ƙasa da ƙasa da ake kira dangane da ‘yancin ɗan Adam.


ALMIZAN: Ta yaya kuke tabbatar da ingancin bayanan da kuke yaɗawa?


KARRAR: Muna tare da kwararrun ‘yan jarida da masana. Ba za mu yaɗa wani labari ba sai mun tabbatar da sahihancinsa daga madogara daban-daban, kuma sau da yawa muna dogaro da shaidun gani-da-ido a rahotanni daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama kamar ‘Human Rights Watch’ da ‘Amnesty International’, da kuma faifan bidiyo daga wurin da abin da ya faru. Har ila yau, muna da hanyoyin tantance labarai da ba sai na bayyana su ga jama’a ba.


ALMIZAN: Ta yaya masu sauraro da al’ummar ƙasa da ƙasa suke karɓar ga abubuwan da kuke yaɗawa?


KARRAR: Lallai akwai gamsuwa dangane da ayyukanmu, kuma ana samun ƙaruwa a yawan masu sauraro da masu bi, musamman daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Shafin ya zama ana ambaton sa a matsayin madogara a cikin rahotanni da taron tattaunawa, kuma akwai ‘yan jarida da suka fara tuntuɓar mu kai tsaye.


ALMIZAN: Menene manyan kulen da kuke fuskanta?


KARRAR: Daga cikin manyan kulen akwai ktsalandan ɗin masu waɗannan manhajoji, inda irin wadannan shafukan ke fuskantar haɗarin hana ko takurawa a wasu ƙasashe. Sai barazanar tsaro ga membobin da ke tafiyar da shafin, musamman waɗanda ke zaune a ƙasashe masu tsanantawa.
Akwai kuma yaƙin da wasu kafofin yaɗa labarai ke yi, inda wasu ƙungiyoyi ke ƙoƙarin ɓata sunan mu ko kuma zarge mu da goyon bayan waɗansu al’umma, duk da cewa duk abin da muke yi shi ne isar da gaskiya da haƙiƙanin zaluncin da ake yi.


ALMIZAN: Daga ƙarshe mi za ka ce ga masu karanta Jaridar Al-Mizan?


KARRAR: Na gode wa Jaridar Al-Mizan saboda ba ni wannan dama da ta yi. Ina kuma ce wa masu karanta ta: Batun gallazawar da ake wa Shi’a Najeriya ba abin da ya shafe su, su kaɗai ba ba ne ba, lamarin ya shafi dukkanin mai rayayyiyar zuciya. Yin shiru game da shi cin mutunci ne ga adalci da ‘yan adamtaka.
Ku kasance da mu a adirenshi Manhajar X: @Najiria_313

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *