Gwamnatin Tarayya Na So A Riƙa Amfani Da Hulɗa da Jama’a Wajen Ƙaryata Cewa Ana Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi A Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga masana harkokin sadarwa da su yi amfani da fayyace gaskiya tare da kafa hujjoji wajen ƙaryata iƙirarin da wasu ke yaɗawa cewa wai ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya.

Idris ya yi wannan kiran ne a Abuja a wajen babban taron ƙaddamar da reshen ƙasar nan na Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a ta Duniya (World Public Relations Forum, WPRF Abuja 2026), inda ya yi gargaɗin cewa martabar ƙasar nan tana fuskantar barazana daga mutanen wasu ƙasashe da ke ƙoƙarin gurɓata gaskiya da raunana haɗin kan ‘yan ƙasa.

Ya ce: “Ya kamata mu fahimci irin barazanar da ke fuskantar martabar ƙasar mu daga wasu maƙaryata da ke ƙoƙarin ɓata sunan Nijeriya, suna yaɗa cewa wai ana yi wa wasu mutane kisan ƙare dangi saboda addinin su. Wannan farfaganda ce da masu ganin haɗin kan mu ya raunana suka kitsa ta daga ƙasar waje.

“Na sha faɗa cewa babu ko ɗigon gaskiya a zancen cewa ana ‘yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi’ a Nijeriya.”

Ministan ya jaddada cewa manufar irin waɗannan labaran ƙaryar ita ce a haifar da rarrabuwar kai, don haka wajibi ne a riƙa mayar da martani ta hanyar sadarwa cikin gaskiya da bin ƙa’idar aikin jarida.

Ya ƙara da cewa, “Ina kira a gare mu da mu yi amfani da dabarun hulɗa da jama’a bisa gaskiya da hujjoji domin mu ƙaryata waɗannan muggan labaran game da Nijeriya.”

Ministan ya ce a wannan zamani na dijital, bayanai suna yaɗuwa cikin sauri fiye da yadda mutane ke nazari, don haka masana harkokin sadarwa su kasance masu gaskiya, tausayi, da sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Ya danganta wannan kira da Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wanda, a cewar sa, yake ƙoƙarin sake gina aminci tsakanin gwamnati da jama’a ta hanyar fayyace gaskiya da hulɗa da jama’a.

A cewar sa, damar da Nijeriya ta samu ta gudanar da Taron Hulɗa da Jama’a na Duniya na 2026 alama ce ta jagorancin Nijeriya wajen sadarwa bisa ƙa’ida da fayyace gaskiya a duniya.

Ya ce: “Wannan taro wata hujja ce cewa ƙarƙashin jagoranci mai hangen nesa na Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Nijeriya ta zama mai murya mafi ƙarfi, mafi haske, kuma mafi ƙarfin hali wajen samar da ingantacciyar sadarwa a Afrika da ma duniya baki ɗaya.”

Idris ya yaba wa Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a da Gudanar da Sadarwa ta Duniya, ƙarƙashin Farfesa Justin Green, da kuma Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), ƙarƙashin Dakta Ike Neliaku, saboda jawo hankalin duniya zuwa ga Nijeriya ta hanyar babban taron na WPRF.

A cikin kira mai cike da bada ƙwarin gwiwa, ministan ya roƙi masana harkokin sadarwa, da ‘yan jarida, da jami’an gwamnati da su rungumi hanyar sadarwa mai ɗauke da fayyace gaskiya da amana.

Ya ce: “Ya dace wannan buɗe taron ya kasance kira ga zukatan mu.
Saƙo ga ƙwararru shi ne: ku tsaya ƙyam kan gaskiya. Saƙo ga ‘yan jarida: ku bayar da rahoto cikin gaskiya da mutunci. Saƙo ga jami’an gwamnati: ku bayyana gaskiya ba tare da ɓoye komai ba. Saƙo ga jama’ar ƙasa: ku yi magana da tunani.”

Ya bayyana tabbacin cewa za a riƙa taron WPRF Abuja 2026 a matsayin muhimmin zango wajen sake gina martabar Nijeriya a idon duniya.

Ya ce: “A ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya na sake fasalta yadda ake kallon ta a idon duniya. Ya dace wannan Taro ya zama abin tunawa a matsayin lokacin da babbar dimokiraɗiyyar Afrika ta jagoranci duniya wajen bayyana ma’anar aikin sadarwa na gaskiya da gaskiya.”

Jigon taron WPRF na bana dai shi ne: “Sadarwa da Gaskiya: Muryar Duniya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *