Shin ya dace Shaikh Masussuka ya amsa muƙabalar da gwamnatin Katsina ta shirya?

Sakamakon koke-koken da Malam Izala ke yawan aikawa game da salon wa’azin Mahaddacin Alƙur’anin nan da ke Katsina, Shaikh Yahaya Masusska, gwamnatin jihar ta sanar da cewa za ta shirya wani zama na musamman domin kowa ya kare kan sa, inda a ƙarshe za a fitar da matsayar za a tilasta wa kowa sai ya bi.

A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar, wacce Daraktan yaɗa labarai na ofishin, Ibrahim Almu Gafai ya sanya wa hannu a yau Talatar nan, ta bayyana cewa tun farko gwamnatin ta tura maganar zuwa gaban mai martaba Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman, CFR domin a yi wa tukka hanci, amma sai abin bai yiwu ba.

A sanarwa, an bayyana cewa “gwamnatin jihar Katsina ta karbi koke-koke game da salon wa’azin Malam Yahaya Masussuka, wanda suka ce ya saba ma koyarwar addinin musulunci.

“Haka kuma gwamnatin ra karbi wani koken daga shi Malam Yahaya Masussuka, inda ya ke kokawa da cewa ‘yan ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a suna zazzagin sa, tare da yi wa rayuwar sa baraza.”

Gwamnatin ta ce, “wannan ne ya sa ta tura wannan magana zuwa masarautar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, CFR.

“Sarkin ya kira duk bangarorin biyu, inda aka tattauna, wanda kuma Sarkin ya hore su da cewa kar wanda ya yi wa’azin da zai cutata wa ɗan uwan sa musulmi.”

Gwamnatin ta ce, amma bayan wannan zaman, ta samu labarin cewa wannan hayaniyar ta ci gaba. “Don haka, saboda da a samu zaman lafiya da fahimtar juna, Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayar da umurnin cewa a sanar da Malam Yahaya Masusska ya shirya kare kan sa bisa zarge-zargen da ake yi masa, zai gurfana gaban wani kwamiti na Malamai, inda za a fitar da tsare-tsre da ƙa’idojin da kowa dole ya bi.

“Za a zauna a fitar da tsayayyun ƙa’idoji, wanda kuma duk wanda ya saba da su, to gwamnati za ta ɗauki tsattsauran mataki a kan sa,” inji sanarwar.

Sai dai wasu da Almizan ta zanta da su kan wannan lamari, sun shawarci Shehin Malamin da kar ya amsa gayyatar zaman yin muƙabalar. Hujjarsu ita ce, irin wannan salo gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin Gwamna Ganduje ta bi ta garƙame Shaikh Abduljabbar bayan an yi masa mummunan ƙazafin zagin Manzon Allah, alhali kowa ya san Shehin Malamin da da’awar kare daraja da martabar Manzo (S).

Suka ƙara da cewa, kamata ya yi Shaikh Masussuka ya garzaya kotu a birnin Katsina, yana mai roƙon kotun ta dakatar da wannan muƙabalar, saboda ana so a hana shi bayyana ra’ayinsa na addini ne kawai.

WATA TA DABAN
Shin ka mallaki littafin Tarihin jaridar ALMIZAN DA GWAGWARMAYARTA?
N1000 kacal ake sai da littafin da marubuta 12 suka yi rubutu a ciki.
Ka tuntubi 08037023343 don ka turo kuɗin, a tura ma littafin ta WhatsApp.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *