CBN ya soke lasin bankuna biyu bayan sun karya ƙa’ida da kasa cika sharuɗɗa

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da gaggauta soke lasin gudanar da hadahadar bayar da ramcen gina gidaje da jingina na ‘Aso Savings and Loans Plc’ da kuma ‘Union Homes Savings and Loans Plc’.

Wannan mataki dai wani yunƙuri ne na ƙarfafa sashen Bankunan Gidaje da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin banki.

Kamar yadda wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta CBN mai riƙo, Hajiya Hakama Ali, ta wallafa a shafin X na bankin a ranar Talata, CBN ya bayyana cewa bankunan sun karya wasu tanade-tanade na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA) ta 2020 da kuma Sabbin Ka’idojin Gudanar da Bankunan Gidaje a Nijeriya.

A kan haka ne Hakama ta ce CBN ya soke lasin domin hakan na daga cikin ci gaba da ƙoƙarin CBN na tabbatar da tsaro da ingancin tsarin banki, kare ajiyar kuɗin abokan hulɗa, da tabbatar da cewa bankuna masu ƙarfi ta fuskar kuɗi kaɗai ke aiki a kasuwar bankunan gidaje.

“Daga cikin laifuffukan da aka gani a fili, akwai gaza cika mafi ƙarancin kuɗin hannun jari da aka tanada, rashin isassun kadarori da za su rufe basussuka, kasancewa cikin matsanancin ƙarancin jari inda ƙimar wadatar jari ta faɗi ƙasa da abin da doka ta tanada, da kuma rashin bin umarnin da CBN ta bayar,” inji bankin.

Daga nan CBN ya jaddada cewa wannan mataki ya dace da aikin sa na tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a tsarin kuɗin ƙasa da kuma kare amincewar jama’a ga sashen banki.

Daraktar Sadarwar ta sake tabbatar da ƙudurin CBN na gina tsarin kuɗi mai ƙarfi da nagarta a Nijeriya.

Bankunan gidaje su ne cibiyoyin kuɗi da ke bayar da ramcen sayen gida da sauran kayayyakin tallafin gidaje, kuma CBN na sanya musu tsauraran ƙa’idoji domin kare abokan hulɗa da tabbatar da kwanciyar hankalin tsarin kuɗi Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *