Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, ya halarci bikin gabatar da littafi da tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya rubuta, mai taken “Kanun Labarai da Taƙaittun Labarai: Muhiman Lokutan Kafofin Yaɗa Labarai da Aka Fayyace Gwamnati” (“Headlines & Soundbites: Media Moments That Defined an Administration”). Littafin yana bayyana ayyukan tsohon Ministan a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Margayi Muhammadu Buhari.

Taron, ya samu halartar iyalan margayi tsohon Shugaban ƙasar da tsofaffin ministoci a lokacin gwamnatin sa, a yau Laraba a Abuja.




