Gwamnatin Tarayya ta haramta karɓar kuɗi domin sanyawa magidanta da ‘yan kasuwa mitar wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya ta haramta karɓar kuɗi domin sanyawa magidanta da yan kasuwa mitar wutar lantarki.

  • Gwamnatin ta yi barazanar hukunci ga duk wanda ya sake siyar da mita ga wani ɗan ƙasa.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta wa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da masu sanya mita karɓar kowanne irin kuɗi daga jama’a kafin ko bayan girke mitar wuta, tare da yin gargaɗin cewa duk jami’i ko mai girke mita da aka kama yana karɓar kuɗi zai fuskanci hukunci.

Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake duba sabbin smart meters da aka shigo da su ƙasar nan a tashar APM Terminals da ke Apapa, Lagos. Ya ce an sayo mitocin ne ƙarƙashin shirin Bankin Duniya na Distribution Sector Recovery Programme (DISREP), kuma wajibi ne a sanya su ga masu amfani da wuta kyauta.

Ministan ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na neman kuɗi daga masu amfani da wuta laifi ne. “Ko jami’an DisCos ko masu sanya mita ba su da ikon karɓar ko sisi guda daga jama’a. Sanya mitocin kyauta ne gaba ɗaya,” in ji shi.

Adelabu ya bayyana farin cikinsa kan shigowar karin mitoci 500,000, inda ya ce gwamnati na shirin shigo da mitoci kimanin miliyan 3.4 a karo na biyu da za a yi. Ya ce a kashin farko na mitoci miliyan 1.43, an riga an karɓi kusan miliyan ɗaya, kuma sama da mitoci 150,000 an riga an sanya su ga magidanta a faɗin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa mitocin za a raba su ga dukkan masu amfani da wuta ba tare da la’akari da band ɗinsu ba, da nufin rage gibin mitoci, inganta adalci da gaskiya wajen lissafin kuɗin wuta, da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga a ɓangaren wutar lantarki.

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta sa ido sosai kan aikin sanya mitocin, tare da buɗe ofishin karɓar ƙorafe-ƙorafe domin jama’a su rika kai rahoton duk wani jami’i ko mai sanya mita da ya nemi kuɗi ba bisa ka’ida ba. Ya ce Hukumar Kula da Wutar Lantarki (NERC) da hukumomin jihohi za su taka rawa wajen sa ido da ɗaukar mataki.

A cewarsa, idan aka kammala wannan shiri, cikin ‘yan shekarun nan kowane gida, kasuwa da ma’aikata za su kasance da mita, lamarin da zai kawo sauyi mai ma’ana a ɓangaren wutar lantarki a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *