CBN ya warware ƙorafe-ƙorafen masu hulɗa da bankuna har 9,771 cikin wata shida

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa ya warware ƙorafe-ƙorafen abokan ciniki ko hulɗa da bankuna 9,771 daga cikin jimillar ƙorafe-ƙorafe 10,704 da aka samu a watanni shidan farkon shekarar 2025.

CBN ta bayyana hakan ne a cikin sabon Rahoton Tsaron Tsarin Hadahadar Kuɗi, inda ya nuna cewa yawan ƙorafe-ƙorafen da aka karɓa a wa watannin Janairu zuwa Yuni ya ƙaru da kashi 143.3 cikin ɗari idan aka kwatanta da guda 4,398 da aka samu a watanni shidan farkon shekarar 2024.

“Jimillar ƙorafe-ƙorafen da bankin ya karɓa sun a ƙaru da kashi 143.38 zuwa 10,704 daga 4,398 da aka samu a watanni shidan ƙarshen shekarar 2024.”

A cewar CBN, wannan ƙarin ya samo asali ne daga dalilai da dama, ciki har da ƙaruwar wayar da kan jama’a da bankin ya karaɗe ɗaukacin jihohin ƙasar nan ya yi, game da haƙƙin masu amfani da bankuna, ƙarfafa dokoki kan rahoton ƙorafe-ƙorafe, da kuma ƙarin amincewar abokan ciniki ga tsarin warware matsaloli da biyan diyya na bankin.

“Binciken ƙorafe-ƙorafen ya nuna cewa kashi 53.45 cikin ɗari an shigar da su ne kan Bankunan Kuɗi na Kasuwanci (CMNBs), yayin da kashi 46.55 cikin ɗari suka shafi Sauran Cibiyoyin Kuɗi (OFIs).

Binciken ya jaddada cewa “sai dai an mayar wa masu ƙorafi naira biliyan 7.17 da dala 3,432.20.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *