Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana musabaha da Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon, Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi, a lokacin ziyarar a ranar 22 ga Janairu, 2026, a Abuja. Hoto daga: Khalid Ahmed
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gyare-gyaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa a fannin ilimi sun riga sun fara samar da damarmaki na gaske ga matasan Nijeriya, tare da tabbatar da samun ilimi, daidaito da kuma inganci a jami’o’in ƙasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja (wadda aka sani da Jami’ar Abuja), Farfesa Hakeem Babatunde Fawehinmi, wanda ya jagoranci manyan jami’an jami’ar zuwa ziyarar ban-girma a ofishin sa.
A cewar Ministan, “Shirye-shirye irin su Asusun Ba da Rance ga Ɗaliban Nijeriya (NELFUND), tallafin ƙirƙire-ƙirƙire ga ɗalibai, da kuma inganta dangantaka tsakanin gwamnati da jami’o’i, sun riga sun fara ƙarfafa fannin ilimi tare da samar da damarmaki na gaske ga matasan Nijeriya.”
Ya ƙara da cewa: “A ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya tana aiwatar da muhimman gyare-gyare a fannin ilimi domin tabbatar da samun ilimi, daidaito, da inganci a dukkan jami’o’in mu.”
Ministan ya kuma jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa haɗin gwiwa da jami’o’in Nijeriya, musamman wajen bunƙasa ilimin kafofin watsa labarai, haɓaka aikin jarida nagari, da kuma tunkarar ƙalubalen yaɗa labaran ƙarya da rashin amfani da fasahar zamani yadda ya dace.
Ya bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci kuma mai ma’ana a wannan lokaci, yana mai cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai cibiya ce da aka sadaukar domin yi wa jama’a hidima wadda ta himmatu wajen tallafa wa cibiyoyin ilimi ta hanyar bayyana su, sadarwa da jama’a, jagoranci, da kuma daidaita manufofi.
Ya tabbatar wa tawagar jami’ar cewa a shirye Ma’aikatar take don ci gaba da haɗin gwiwa da haɗaka mai ɗorewa.
Ministan ya jinjina wa Jami’ar Yakubu Gowon bisa kafa Sashen Nazarin Kafofin Watsa Labarai da Sadarwa, yana mai bayyana rarrabe karatun Mass Communication zuwa fannoni na musamman a matsayin abin da ya dace da tsarin duniya.
Ya jaddada buƙatar ƙarin hulɗa tsakanin ƙwararrun ’yan jarida da ɗalibai domin cike giɓin da ke tsakanin karatun aji da aikace-aikacen zahiri.
Ya kuma bayyana jagorancin Gwamnatin Tarayya wajen bunƙasa ilimin kafofin yaɗa labarai da bayanai, inda ya ambaci yadda Nijeriya ta karɓi baƙuncin Cibiyar UNESCO ta Ilimin Kafofin Watsa Labarai (IMILI)–wadda ita ce irin ta ta farko a duniya—a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙi da labaran ƙarya da ƙarfafa amincewar jama’a ga labaran da suke samu.
Tun da farko, Shugaban jami’ar, Farfesa Fawehinmi, ya taya Ministan murna bisa jagorancin sa a fannin yaɗa labarai, sannan ya nemi goyon baya, haɗin gwiwa, da jagoranci daga Ma’aikatar ga Sashen Nazarin Kafofin Watsa Labarai da Sadarwa gabanin tantance shi.
Ya kuma bayyana shirye-shiryen jami’ar na mara wa shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya da manufofin ta baya.
