NAZARI: Yadda shirin CBN na ƙarfafa jarin bankuna zai fara samar da gagarimin tattalin arziki tun daga 2026

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Yanzu haka dai Babban Bankin Nijeriya (CBN) a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Olayemi Cardoso na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kyakkyawan tsari da ƙa’idoji tare da ƙarfafa tsarin kuɗin Nijeriya, shirin sake ƙarfafa jarin bankuna da ake aiwatarwa na nuna aniyar CBN wajen kafa tsarin kuɗi mai ƙarfi da juriya, wanda zai iya tallafa wa burin Nijeriya na samar da tattalin arziki mai darajar dala tiriliyan ɗaya.

Domin cimma tsarin kuɗi mai ƙarfi da juriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN) bai gajiya ba wajen jagorantar shirin sake ƙarfafa jarin bankuna ta hanyar ganin bankuna sun ninninka jarin su. Tun a ranar 28 ga Maris, 2024, CBN ya sanar da shirin sake ƙarfafa jarin bankuna na tsawon shekaru biyu, wanda ya fara aiki daga 1 ga Afrilu, 2024. Shirin ya tanadi mafi ƙarancin jari na naira biliyan 500 ga bankunan kasuwanci masu lasisin kasa da kasa, naira biliyan 200 ga masu lasisin ƙasa baki ɗaya, da kuma naira biliyan 50 ga bankunan yankuna. Lokacin cika waɗannan sharuɗɗa na watanni 24 zai ƙare a ranar 31 ga Maris, 2026.

Fitowar manyan bankuna masu ƙarfi na daga cikin babbar ribar da ake sa ran samu daga wannan shiri.
Babban bankin, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Olayemi Cardoso, na da ra’ayin cewa samun ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa na buƙatar cikakken goyon baya daga tsarin kuɗi. Saboda haka, CBN na ƙoƙarin daidaita manufofin kuɗi da na kasafin kuɗi domin cimma hangen nesa na gwamnati na bunƙasar kasuwanci da kuma gina tattalin arziki mai darajar dala tiriliyan ɗaya.

A cewar Cardoso, babban burin jagorancin CBN shi ne kare tsarin kuɗin Nijeriya tare da tabbatar da ƙarfin sa da sahihancin sa a cikin gida da ƙasashen waje, ta hanyar ƙarfafa tsarin bin doka da ƙa’ida da kuma inganta tsarin kula da ƙoƙarin kauce wa barazanar cikas. Don cimma wannan buri, CBN ya sake jaddada ƙudurin sa na tabbatar da tsarin kuɗi mai gaskiya da juriya, ta hanyar tsaurara bin ƙa’idojin doka da inganta kula da haɗari a dukkan cibiyoyin kuɗin Nijeriya.

Tantance Ci Gaban Sake Ƙarfafa Jari

Kafin wa’adin ranar 31 ga Maris, Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Manufofin Tattalin Arziki, Dakta Muhammad Abdullahi, ya bayyana a ranar Alhamis, 15 ga Janairu, a wani taron Ƙungiyar Tattalin Arzikin Nijeriya (NESG) a Legas, cewa bankuna 20 sun riga sun cika sabbin sharuɗɗan jari.

A tuna cewa a taron ƙarshe na Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) na shekarar 2025, Cardoso ya bayyana cewa bankuna 16 sun riga sun cika dukkan sharuɗɗan sabbin ƙa’idojin jari kafin wa’adin ƙarshe. Bayanin Abdullahi ya nuna ci gaba mai kyau a ƙoƙarin CBN ƙarƙashin jagorancin Cardoso na kafa tsarin banki mai ƙarfi da juriya a ƙasar.

A halin yanzu, Nijeriya na da bankuna 44 masu karɓar ajiya a rukunoni daban-daban na lasisi. Yayin da wa’adin ke ƙaratowa, wakilin mu ya ji cewa aƙalla bankuna bakwai na duba yiwuwar rage lasisin su daga na ƙasa baki ɗaya zuwa na yankuna, la’akari da inda ayyukan su suka fi mayar da hankali da kuma irin damar da fasahar bankin zamani ta dijital ke bayarwa a faɗin ƙasar.

Haka kuma, an gano cewa wani banki mai lasisin ƙasa da ƙasa ya nuna a ‘yan kwanakin nan cewa yana iya rage lasisin sa zuwa na ƙasa baki ɗaya kafin wa’adin ƙarshe, yayin da yake ci gaba da ƙoƙarin ƙara jarin sa domin sake samun lasisin ƙasa da ƙasa.

CBN na rarraba bankuna zuwa rukuni uku – na kasa da kasa, na ƙasa baki ɗaya, da na yankuna – bisa ƙarfin su na kuɗi. A ƙarƙashin ƙa’idojin sake ƙarfafa jari, baya ga tara kuɗi, dole ne bankuna su gabatar da sabbin kuɗaɗen jarin su domin tantancewa kafin a amince da rabon hannun jari da sakin kuɗin don kammala aikin tayin da ƙara sabon jari a asusun jarin bankin.
CBN ne ke da sa hannun ƙarshe a kwamitin tantance jarin bankuna mai mambobi uku, wanda ya haɗa da Hukumar Kula da Kasuwar Hannun Jari (SEC) da Hukumar Kula da Inshorar Ajiya ta Nijeriya (NDIC). Aikin kwamitin shi ne duba da tantance sabbin kuɗaɗen da bankuna ke tarawa a ƙarƙashin shirin sake ƙarfafa jarin bankuna.

Sabon Jari Zai Kai Naira Tiriliyan 4.14

A cikin wani rahoto mai taken “Kalubalen Tattalin Arziki na Nijeriya Sun Haifar da Sake Ƙarfafa Jarin Bankuna”, kamfanin Deloitte ya kiyasta cewa jimillar kuɗin da za a tara a wannan shiri zai kai naira tiriliyan 4.14.

Rahoton ya ce ƙara mafi ƙarancin jarin bankuna daga naira biliyan 50 zuwa naira biliyan 500, gwargwadon nau’in lasisi, mataki ne mai matuƙar muhimmanci domin ƙarfafa isasshen jari a ɓangaren kuɗin Nijeriya. Rahoton ya kuma bayyana cewa isasshen jarin bankunan Nijeriya ya samu tasiri sosai daga kalubalen tattalin arziki kamar hauhawar farashi da ribar banki, sauyin darajar kuɗi, da ƙarancin musayar kuɗaɗen waje.

“Ƙarin jarin zai tabbatar da cewa bankunan Nijeriya na da ikon ɗaukar manyan ƙalubale da kuma tsayawa daram a lokacin girgizar tattalin arziki ta cikin gida da ta waje. Hakan kuma zai ƙara yawan kuɗin da ke hannun bankuna, wanda zai faɗaɗa ikon su na ɗaukar asara,” inji rahoton.

Yayin da ake sa ran tara sabon jari na naira tiriliyan 4.14, kuma bankuna 20 sun riga sun cika mafi ƙarancin sharuɗɗan jari, ana sa ran wannan shekara za ta zama muhimmin mataki a tattalin arzikin ƙasa.

A sabuwar sanarwar sa kan shirin sake ƙarfafa jari a watan Disambar 2025, Cardoso ya bayyana cewa CBN zai tsaurara tsarin shugabanci nagari, ƙara gaskiya, da ƙarfafa ɗaukar alhaki domin kare kuɗaɗen da aka tara. Ya kuma ce yayin da wasu bankuna sun riga sun cika sabbin sharuɗɗan jari, sauran suna samun ci gaba sosai kuma suna da kwarin gwiwar cika sharuɗɗan kafin ranar 31 ga Maris, 2026.

“Bankunan da suka cika ko suka wuce sabbin sharuɗɗa hujja ce bayyananniya ta zurfi, juriya, da ƙarfín tsarin bankin Nijeriya,” cewar Cardoso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *