An Binne Gawar Marigayi Buhari A Gidan Sa Da ke Daura, Jihar Katsina

An binne gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina, a safiyar yau, cikin jimami da addu’o’i daga iyalansa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, ministoci, da dubban jama’a daga sassa daban-daban na ƙasa da waje.

Jana’izar marigayin ta samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, shugaban ƙasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló, da Firayim Ministan Jamhuriyar Nijar, Ali Lamine Zeine.

Sauran manyan baki sun haɗa da shugabannin rundunonin tsaro, shugabannin masana’antu, Ministoci, tsofaffin gwamnoni, wakilin shugaban ƙasar Chadi, malamai, da fitattun mutane daga cikin gida da waje. Kafin binne gawar, dakarun haɗin gwiwar sojoji sun gudanar da harbe-harben ban girma sau 21 a matsayin girmamawa ta ƙarshe ga marigayin.

Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, shi ne ya karanta tarihin rayuwar Buhari, inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Najeriya da iyalansa. Ya ce marigayin soja ne nagari mai cikakken kwazo, gaskiya, da kishi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar ƙasa da kyakkyawan shugabanci.

A lokacin da aka iso Daura da gawar, dubban jama’a ne suka taru suna Kabbara da addu’ar rahama ga marigayin. Iyalansa sun samu damar duban gawarsa na ‘yan mintoci kaɗan don yin addu’ar karshe kafin a rufe shi kabarinsa.

Marigayi Muhammadu Buhari ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban soja daga 1984 zuwa 1985, sannan ya sake komawa mulki ta hanyar zabe a 2015, kuma aka sake zaɓensa a 2019. Mulkinsa ya shahara da yaƙi da cin hanci, manyan ayyuka raya kasa, da kuma shan ƙalubale a fannonin tsaro da ci gaban tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *