Ashafa Murnai Barkiya
Malejin hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.45 cikin 100 a watan Nuwamba 2025, abinda ke nuna ci gaba da samun sauƙin tashin farashi da rangwamen tsadar rayuwa, daidai lokacin da ake bankwana da shekarar 2025.
Hakan kuwa nuni ce tare da ƙarfafa tsammanin cewa matakan tsauraran manufofin kuɗi da gyare-gyaren kasuwar canjin kuɗaɗe da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ɗauka sun fara haifar da sakamako nagartacce.
Wannan adadi na kashi 14.45 na nuna an samu ragin maki 1.6 idan aka kwatanta da kashi 16.05 cikin 100 da aka samu a watan Oktoba 2025, kamar yadda bayanan da Hukumar Kididdiga Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar a ranar Litinin suka nuna.
Sabbin bayanan sun nuna ɗaya daga cikin wannan ragin hauhawar farashi na wata-wata a bana, bayan tsawon lokaci na tsadar rayuwa da hauhawar farashi da sauye-sauyen darajar kuɗi da tsadar abinci suka haddasa.
NBS ta bayyana cewa wannan ragi yana nuna a hankali ana samun sauƙin hauhawar farashi a muhimman sassan tattalin arziki, duk da cewa har yanzu ana fuskantar wasu matsin farashi na asali a wasu kayayyakin.
A bisa ƙididdigar wata-zuwa-wata, hauhawar farashi ya kai kashi 1.22 cikin 100 a watan Nuwamba 2025, idan aka kwatanta da kashi 0.93 cikin 100 watan Oktoba 2025.
Hukumar ta yi bayani da cewa, duk da cewa matsalar hauhawar farashi na raguwa idan paka duba a shekara-shekara, saurin ƙarin farashin kayayyaki a cikin watan ya ɗan fi na watan da ya gabata.
“Dangane da bambancin tashin farashi ko raguwar sa daga wata-zuwa-wata, hauhawar farashi a watan Nuwamba 2025 ya kai (kashi 0.93 cikin 100) da kashi 0.29 cikin 100,” cewar NBS.
“Wannan na nufin cewa a watan Nuwamba 2025, malejin haihuwar farashi ya sauka ƙasa da wanda aka samu a watan Oktoba 2025.”
Dalla-dallar bayanan ta nuna raguwar hauhawar farashi sosai a birane, inda hauhawar farashin birane ta kai kashi 13.61 cikin 100 a shekara-shekara a watan Nuwamba 2025.
Wannan na nuni da ragin maki 23.49 idan aka kwatanta da kashi 37.10 cikin 100 da aka samu a watan Nuwamba 2024.
A ƙididdiga ta wata-zuwa-wata, hauhawar farashi a birane ta ragu zuwa kashi 0.95 cikin 100, daga kashi 1.14 cikin 100 a watan Oktoba 2025. Matsakaicin hauhawar farashi a birane na watanni 12 ya ragu zuwa kashi 20.80 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 35.07 cikin 100 a daidai wannan lokaci na 2024.
Haka kuma, hauhawar farashi a karkara ya ragu matuƙa, inda adadin shekara-shekara ya sauka zuwa kashi 15.15 cikin 100 a watan Nuwamba 2025, ragin maki 17.12 daga kashi 32.27 cikin 100 da aka tabbatar a watan Nuwamba 2024.
Yayin da ‘yan Najeriya ke bankwana da shekarar 2025, farashin kayan abinci na ci gaba da sauka, ta yadda a kasuwannin sayar da amfanin gona a Arewacin Nijeriya an riƙa sayar da buhun masara sabuwa da buhun sabuwar dawa, har ƙasa da naira dubu ashirin.
Hakan na nuni da cewa masu ƙaramin ƙarfi za su ci gaba da sayen abincin da ake nomawa a cikin gida a farashi mai sauƙi.
