CBN ya gindaya sabbin ƙa’idoji da sharuɗɗan amfani da P.O.S

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) gindaya sabbin sharuɗɗa da ƙa’idojin amfani da P.O.S a hada-hadar kuɗaɗe ta yau da kullum.

Daga cikin sabbin ƙa’idojin, an gindaya cewa ba a yarda ejan masu tiransifa da P.O.S su zarce tiransifa ta sama da Naira miliyan 1 da dubu 200 ba (N1.2m) a duk P.O.S ɗaya a kowace rana.

Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar Talata, ya ce an fito da sabbin sharuɗɗan domin tabbatar da sa-ido da kuma inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe.

Sanarwar wadda Daraktan Kula da Tsare-tsaren Biyan Kuɗaɗe, Musa Jimoh ya sa wa hannu, ya ce hakan zai sa tsarin hada-hadar kuɗaɗe na zamani ya kare kwastomomi sosai daga faɗawa tsilla-tsillar matsalolin yau da kullum da suke fuskanta a tsarin tiransifa ta P.O.S.

Ya ce kuma wajibi ne dukkan bankuna su riƙa bada rahotonannin hada-hadar kuɗaɗen da ejan-ejan ɗin su suka yi da P.O.S, domin ƙarƙafa sa-ido a tsarin hada-hadar tare da inganta shi.

Yayin da sanarwar ta fara aiki nan take, ta kuma ƙara da cewa daga 1 ga Afrilu, 2026 za a tabbatar ana bada bayanan daidai wurin da kowane mai P.O.S ke zaune.

“Dukkan bankuna da masu ruwa da tsaki na cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe su tabbatar da cewa ana bin waɗannan sabbin sharuɗɗa waɗanda CBN ya gindaya.”

A ƙarƙashin wannan sabon tsari, tilas ejan ya riƙa hada-hadar kuɗaɗe da P.O.S ta hanyar amfani da asusun banki da ya ware musamman domin hada-hadar ko kuma ‘Asusun Tafi da Gidan Ka’ na ‘wallet’ daga wata cibiyar hada-hadar kuɗaɗe ta zamani, domin tabbatar da samun sauƙin sa-ido da bibiyar abin da ke gudana.

CBN ya yi gargaɗin cewa wanda ya yi amfani da asusun da ba shi aka tantance masa ba, to shi wannan ejan ɗin ya karya ƙa’idar da tilas sai an hukunta shi.

Duk ejan ɗin da aka samu da laifin zamba, rashin bin ƙa’ida, ko wasu laifukan da dokar hada-hadar kuɗi ta haramta, to za a sa-ido a kan sa, kuma a soke yarjejeniyar da aka ƙulla da shi.

An kuma umarci cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe su buga sunayen dukkan ejan-ejan ɗin su a shafin su na intanet, tare da rubuta sunayen dukkan rassan da ejan-ejan ɗin ke ƙarƙashi.

Manyan ejan-ejan, wato ‘Super Ejan’ tilas ya kasance akwai aƙalla ejan guda 50 a ƙarƙashin kowane ‘Babban Ejan’, a faɗin shiyyoyin ƙasar nan shida. Yin hakan zai tabbatar da kowane lungu ya samu damar yin hada-hadar kuɗaɗe ta zamani kuma a sauƙaƙe.

Wasu daga cikin sharuɗɗan kuma sun haɗa da cewa: “An hana ejan mai amfani da na’urar P.O.S sauya wurin zama, matsawa nesa ya yi tirasifa ko rufe wurin hada-hadar sa ba tare da neman izni daga Babban Ejan ba.

“Duk ejan ɗin da zai canja wurin zama, tilas ya manna sanarwar yin haka a wurin da yake hada-hada, tun kwanaki 30 kafin zuwan ranar da zai canja wuri.

An kuma buƙaci cibiyoyi ko kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe su fito da wani tsarin amfani da na’urorin da za su riƙa maida wa kwastoma kuɗaɗen sa, nan take idan aka cire, amma ba su je inda aka tura ba, bayan an rigaya an cire masa.

Tilas a riƙa ajiye rasiɗin aikawa ko cirar kuɗi mai ɗauke da sunan ejan ɗin da shiyyar da yake, har tsawon shekaru biyar.

CBN ya ce an fito da sabbin sharuɗɗan domin inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe, sa-ido tare da tabbatar da jama’a da dama na samun yin hada-hada cikin sauƙi a kowane lungu suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *