CBN ya yi farin cikin cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa cire sunan Nijeriya daga ƙasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffar hada-hadar kuɗaɗe da su a duniya cewa, hakan tabbaci ne da ke nuna duniya ta gamsu da tsare-tsaren tattalin arzikin da wannan gwamnati ta bijiro da su.

Cikin wata sanarwar da Daraktar Riƙon Sashen Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai, Hakama Sidi Ali ta sa wa hannu kuma ta fitar a ranar Asabar, ta nuna cewa duniya ta gamsu da tsare-tsaren harkokin kuɗaɗe da kuma gagarimin yaƙi da almundahanaha da zambar kuɗaɗen da ake kan yi a Nijeriya.

CBN ya ci gaba da cewa an cire Nijeriya daga ƙasashen da FATF ke sa-ido kan su, bayan kwamitin sa-ido ɗin ya gani tare da tabbatarwa irin “gagarimin ci gaban” da Nijeriya ta samu wajen yi wa tsare-tsaren kuɗaɗe ragama da linzamin daƙile zambar kuɗaɗe da kuma datse hanyoyin safarar kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.

FATF dai ƙaƙƙarfar hukumar sa-ido ce ta duniya wadda ke lura kan hada-hada da harƙallar kuɗaɗe ta ɓarauniyar hanya. Ta bayyana cire sunan Nijeriya a ranar Juma’a, tare da ƙasashen Afrika ta Kudu, Mozambique, Burkina Faso.

Hakama Ali ta ci gaba da cewa cire sunan Nijeriya ya nuna irin kyakkyawan tasirin da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da CBN, Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Lura da Hada-hadar Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) da kuma EFCC suka yi.

“Rawar da CBN ya taka wajen samun wannan nasara ta shafi tabbatar da sa-ido sosai, tsara ƙa’idoji, gindaya sharuɗɗ da gudanar da ayyuka ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen hada-hadar kuɗaɗe.”

Daga cikin tsare-tsaren da FATF tare da Kafofin Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe na Afrika ta Yamma su ka yi wa bin diddigi, akwai tsarin lambobin sirrin bibiyar Tsarin Musayar Kuɗaɗe, wadda aka ƙirƙiro domin rage harƙalla a hada-hadar musayar kuɗaɗe.

Cire Nijeriya daga ƙasashen da ake kaffa-kaffa da su ɗin zai ƙara cire shakku kan Nijeriya, tare da faɗaɗa hada-hadar cinikayya tsakanin ƙasar da ƙasashen waje, cibiyoyi da masu zuba jari. Haka bankuna za su samu ƙarin hulɗoɗi da masu son haɗin gwiwa daga waje.

An dai saka sunan Nijeriya cikin kasashen da ake sa-ido da kaffa-kaffa da su a cikin 2021, bayan duniya ta nuna rashin amincewa dangane da yadda salon yaƙi da zambar kuɗaɗe ke gudana, musamman wajen matsalar yadda ake samun safarar muggan kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *