Dalilan da Suka Haifar da Jan-ƙafa Wajen Aiwatar da Ayyukan Kasafin 2024 da na 2025 -Yakubu

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Darakta a Ofishin Kasafin Kuɗaɗen Tarayya, Tanimu Yakubu, ya bayyana wa Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Darattawa dalilan da suka haifar da samun Jan-ƙafa wajen kammala aiwatar da ayyukan kasafin kuɗaɗe na shekarar 2024 da na 2025.

Da yake jawabi a gaban kwamitin a ranar Alhamis, a Majalisar Dattawa, Abuja, Yakubu ya ce ƙoƙarin aiwatar da ayyukan kasafin 2024 da na 2025 ya haɗu da tangarɗa, inda ƙwararren masanin tattalin arzikin ya ci gaba da cewa an samu naƙasu da ƙarancin kuɗaɗen shigar da aka yi hasashen samu a lokacin da ake tsara kasafin kuɗaɗe.

“Shekarar ta kasance mana da tsauri sosai, ta yadda yawancin hasashen geji da mizanin awon da muka yi wa kasafin 2024 da na 2025, ya zo ƙasa sosai da yadda muka zata,” inji Yakubu.

Ya ƙara da cewa mizanin awon farashin ɗanyen mai da suka tsara kasafin da shi na Dala 75 ($75) kowace ganga, bai ɗore ba. Ya ce farashin gangar ɗanyen mai ya riƙa sauka da $10 har da $15 ƙasa da mizanin awon kasafin kuɗaɗe.

Yakubu ya alaƙanta wannan giluniya da farashin ya riƙa yi cewa matsala ce da ta shafi duniya, ba Najeriya kaɗai ba.

Babban Darakta ya ƙara bayar da dalilin tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyaki suka haifar da cikas. Sannan ya haddasa ƙarin yawan basussukan kuɗaɗen da Najeriya ke biya, wanda hakan ya riƙa haifar da rashin yawan kuɗaɗen da za a aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da su.

Yakubu ya ci gaba da cewa sabbin dokokin da ke shimfiɗe cikin Dokar Man Fetur ta PIA ta 2022, sun rage yawan kuɗaɗen shigar da Gwamnatin Tarayya ke samu.

Yakubu ya ci gaba da cewa, “A ƙarƙashin Dokar Fetur ta PIA, ana bada kashi 30 na kuɗaɗen shiga na fetur akan ladar gudanar da harkokin dillancin man Najeriya ga NNPC Limited. Sai kuma wani 30 na ribar ɗanyen mai da gas shi ma yana tafiya wajen aikin haƙar mai da iskar gas a wasu wurare da ba su da tabbas, ko haƙar ma’adanan na da wasu matsaloli da ya buwayi yin haka. Yayin da kuma Gwamnatin Tarayya ke ɗauke da nauyin tafiyar da ayyukan NNPC,” inji Yakubu.

“Saboda haka wannan ya haddasa datse yawan kason kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke samu da kusan kashi 70.”

Ya ƙara bayar da dalilin yadda adadin yawan ɗanyen mai da aka riƙa haƙowa ya gaza kai adadin yawan wanda aka yi hasashen samu. Wannan a cewar babban daraktan ya takure kuɗaɗen shiga tare da kawo tsaiko wajen biyan kuɗaɗen manyan ayyuka.

A taron dai Ministan Harkokin Kuɗaɗe, kuma Ministan Lura da Tattalin Arziki, Wale Edun da Akanta Janar na Tarayya, Samsuddeen Ogunjimi duk sun yi jawabai dangane da batun kasafin.

A nasa jawabin bayan taron, Shugaban Kwamitin Kuɗaɗe na Majalisar Darattawa, Sanata Mohammed Sani Musa, ya bayyana wa manema labarai dakatar da gabatar wa Majalisa sabon kasafi har sai an fara gabatar wa majalisar da cikakkun bayanan kasafin 2024 da na 2025 a ranar 23 ga Satumba, 2025 tukunna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *