Farashin abinci na ƙara sauƙi a Najeriya yayin da gwamnati ke samun cigaba a fannin tattalin arziki
Rahotanni daga jihohin Arewa maso Yamma na nuna cewa farashin kayan abinci ya fara raguwa a kasuwanni sakamakon girbin damina mai albarka da manoma suka samu a bana. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da manufofin tallafawa harkar noma da kuma tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
A jihohin Kaduna, Kano da Katsina, manoma sun tabbatar da cewa an samu kyakkyawan girbi na hatsi, tumatir, dawa, gero da shinkafa, abin da ya janyo farashin kayan abinci ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
A kasuwannin Kaduna misali, buhun shinkafa na kilo 50 da ake sayarwa a kan Naira 100,000 a baya, yanzu ya koma tsakanin Naira 50,000 zuwa Naira 63,000. Haka kuma farashin kwandon tumatir ya sauka daga Naira 120,000 zuwa Naira 35,000.
Wani ɗan kasuwa a Dawanau, Alhaji Bala Ali, ya tabbatar da cewa “yawan amfanin gona daga kauyuka ya ƙaru sosai, abin da ya taimaka wajen daidaita farashin abinci da kuma tabbatar da wadatar kayan masarufi a kasuwa.”
A jihar Kano, rahotanni sun ce yawancin manoma sun samu gagarumin girbi saboda yanayin ruwan sama da ya yi daidai da lokacin noma. Wasu manoma ma sun yaba da shirin Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) da suka ce ya taimaka wajen samun iri da dabarun noma na zamani.
Wani manomi a Bebeji, Malam Audu Muzammil, ya ce, “Ruwan sama ya yi wadata kuma kwari sun yi ƙasa matuƙa. Daman abinda ya rage mana shi ne adana kayanmu yadda ya kamata. Amma girbi ya yi albarka sosai.”
A jihar Katsina kuwa, duk da cewa wasu manoma sun koka da tsadar takin zamani, suna murna da cewa farashin kayan abinci ya ragu, abin da ya sa mutane da dama ke iya siyan abinci cikin sauƙi.
Malam Kabir Sabiu, wani manomi daga Katsina, ya ce “duk da cewa mun yi asara saboda farashi ya fadi, muna godewa Allah saboda jama’a da dama yanzu suna iya siyan abinci cikin rahusa. Wannan ma wata ni’ima ce.”
Masana tattalin arziki na cewa wannan saukin farashin abinci alama ce ta daidaituwar kasuwa da kuma nasarar da ake samu daga manufofin gwamnati na inganta noma, samar da kayan aikin gona da kuma rage dogaro da abinci daga ƙasashen waje.
Gwamnati dai ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafawa manoma ta hanyar samar da kayayyakin ajiyar amfanin gona, rarraba iri da takin zamani a farashi mai rahusa da kuma inganta tsaro a yankunan karkara domin karfafa noman cikin gida.
Da dama daga cikin ‘yan kasa sun bayyana farin ciki da saukar farashin kayan abinci, musamman bayan dogon lokaci da ake fama da hauhawar farashi.
“Yanzu muna ganin canji a zahiri,” in ji wata magidanciya a Kano, Hajiya Fatima Sani.
“Tumatir, shinkafa, wake, duk sun yi sauƙi. Allah ya kara albarka ga manoma da gwamnati.” Inji ta.
Masu lura da al’amuran tattalin arziki na cewa idan gwamnati ta ci gaba da wannan tsarin, akwai yiwuwar farashin abinci zai ci gaba da daidaituwa kuma hakan zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki ga ‘yan ƙasa.





