
Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki kan tsare-tsare na musamman domin tabbatar da cewa sabbin taraktocin Belarus da aka ajiye za su amfanar da kananan manoma a faɗin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya kaddamar da taraktoci 2,000 da kuma sama da kayan aikin noma na zamani 9,000 a ranar 23 ga Yuni, domin bunƙasa noma a kan sama da hekta 550,000 na filayen noma a ƙasar.
Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Abdullahi, ne ya bayyana haka a Abuja a gefen bikin Ranar Abinci ta Duniya ta bana.

Sanata Abdullahi ya ce shugaban ƙasa ya bada umarnin cewa taraktocin ba za su zama mallakar wasu ‘yan tsiraru ba, ko kuma su shiga hannun da ba su dace ba.
“Mun samu umarni kai tsaye daga shugaban ƙasa cewa mu tsara wani shiri da zai baiwa manoma kanana damar samun amfani da wadannan taraktoci ta hanyar cibiyoyin gudanar da noman zamani da ake shirya kafa wa.”
“A halin yanzu mun kai matakin karshe, kuma muna so mu tabbatar cewa kafin kakar damina ta gaba, wadannan taraktocin sun isa hannun manoma,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa sabbin taraktocin na ɗauke da fasahar zamani wacce ke ba da damar lura da yanayinsu ta hanyar tsarin fasaha.
Ministan ya ce akwai shirye-shiryen horaswa da kuma samar da sassan gyara domin tabbatar da dorewar amfani da na’urorin, tare da bai wa matasa damar koyon amfani da su.
“Muna son mu tabbatar cewa wadannan taraktocin za su kasance masu amfani na dogon lokaci. Za mu horar da matasa kan yadda ake amfani da su, kuma akwai tanadin sassan gyara domin kula da su yadda ya kamata,” in ji Abdullahi.
A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a tura taraktocin zuwa cibiyoyin gudanarwa na noman zamani domin baiwa manoma kanana damar yin noma cikin sauƙi da araha.
An bayyana wannan shiri a matsayin wani yunkuri na gwamnati wajen rage wahalar aikin gona, ƙara yawan amfanin gona, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa da mata a ƙasar.
Rahoton ya kuma nuna cewa ana sa ran shirin zai taimaka wajen samar da sama da tan miliyan biyu na abinci mai gina jiki a duk faɗin ƙasar.
