Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a na Ƙasa, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kammala fiye da ayyuka 500 a fannin lafiya cikin shekaru biyu kacal.
Farfesan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da Cibiyar Kula da Cututtukan Daji (Oncology Centre) ta zamani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) da ke Jihar Edo.
Ya ce wannan ci gaba da aka samu a cikin dan kankanin lokaci alama ce ta canji daga magana zuwa aiki a harkar lafiya, yana mai jaddada cewa tsarin kiwon lafiya a Najeriya na samun gagarumin sauyi.
“A cikin shekaru biyu, mun fara gina sabon tarihin gyaran tsarin lafiya a Najeriya,” in ji Farfesa Pate.
A cewar Minista Pate, gwamnatin tarayya ta aiwatar da ayyuka 501 a asibitoci 61 dake manyan matakai a fadin ƙasar, sannan ta farfado da cibiyoyin lafiya na matakin farko (Primary Healthcare) da dama a ciki har da waɗanda ke jihar Edo.
“Shugaba Tinubu ya zabi fannin da ke shafar rayuwar talaka kai tsaye, kuma ya tabbatar da cewa za a ji tasirin hakan. Wannan matakin gyara da aka ɗauka bai taɓa faruwa ba a baya,” in ji shi.
Farfesa Pate ya kuma bayyana nasarorin da ake samu daga gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, wanda ya ce hakan ya buɗe damammakin kashe kuɗi a bangarorin inganta ilimi da lafiya.
“Saboda gyaran da aka yi, yanzu muna da isasshen ɗamarar saka hannun jari a fannin kiwon lafiya da na ilimi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samu ragi na kashi 30% wajen siyan kayayyakin aikin cibiyoyin cutar daji daga masana’antun duniya, wanda hakan ya sauƙaƙa kashe kuɗaɗen jama’a da yawa.