Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da rage kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026 ga mahajjata daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu sauƙin kuɗi idan aka kwatanta da na bara.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, an bayyana cewa mahajjata daga yankin Borno da Adamawa za su biya Naira miliyan 7,579,020.96, maimakon Naira miliyan 8,327,125.59 da suka biya a 2025, ragun da ya kai Naira 748,104.63.
Haka kuma, masu niyyar tafiya daga yankin Arewa za su biya Naira miliyan 7,696,769.76, wanda ke nuna ragin Naira 760,915.83 daga kuɗin bara da ya kai Naira miliyan 8,457,685.59.
A ɓangaren masu tafiya daga Kudancin ƙasar kuwa, farashin da aka sabunta na 2026 shi ne Naira miliyan 7,991,141.76, raguwar Naira 792,943.83 daga kuɗin 2025 da ya kai Naira miliyan 8,784,085.59.
Hukumar ta ce wannan ragin kuɗi na zuwa ne sakamakon ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa suke yi domin sauƙaƙa wa alhazai, tare da tabbatar da cewa farashin bai zama cikas ga masu niyyar gudanar da ibadar Hajji ba.
NAHCON ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da shirin Hajji na 2026 ya gudana cikin nasara da tsari.
