Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Gidaje 200 Ga ’Yan Gudun Hijira a Jihar Kebbi A Ƙarƙashin Hukumar NEMA, domin rage musu radadin rashin matsuguni da suka samu sakamakon ƙalubalen da suka fuskanta.
Babbar Daraktar Hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce ta sanar da hakan yayin kaddamar da raba kayan agaji ga mutanen da ibtila’i ya shafa a Birnin Kebbi, ranar Juma’a.
Hajiya Zubaida ta bayyana cewa lamarin ambaliyar ruwa, guguwar iska da ruwan sama mai ƙarfi da suka shafi ƙananan hukumomin Shanga, Suru, Bunza, Danko-Wasagu, Koko-Bese da Augie sun bar ɗaruruwan mutane ba matsuguni. Ta ce shirin samar da gidajen da gwamnatin tarayya ke yi, karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na “Renewed Hope” zai bada gudunmawa wajen ceto rayuka da dawo da martabar al’umma.
Ta kuma tabbatar da cewa hukumar NEMA za ta cigaba da aiki tare da gwamnatin jihar don tabbatar da jin daɗin ’yan kasa da inganta rayuwa.
Gwamna Jihar Kebbi, Nasir Idris ya gode wa hukumar bisa jajircewar ta, tare da bayyana cewa jihar ta kafa kwamiti tun a shekarar 2024 don wayar da kai ga mazauna yankunan da ambaliya ke yi wa barazana. Ya kuma bukaci hukumar da ta sanar da gwamnatin jihar lokacin da za a fara ginin gidaje 200 domin a haɗa gwiwa wajen tabbatar da nasara.