ALMIZAN -Since 1991

A Hausa Newspaper for the Hausa speaking people in Nigeria and diaspora.

Labarai

Hukumar NELFUND ta raba fiye da Naira biliyan 116 ga ɗalibai sama da dubu 600 tun bayan ƙaddamar da shirin lamunin a Najeriya

Hukumar bayar da lamunin karatu ta Najeriya (NELFUND) ta ce ta raba sama da Naira Biliyan 116.4 ga dalibai fiye da 624,000 tun bayan kaddamar da shirin lamunin karatu a ranar 24 ga Mayu, 2024.

A cewar rahoton da hukumar ta fitar a shafinta na X (Twitter) a ranar Talata, 28 ga Oktoba, NELFUND ta karɓi fiye da rejistar ɗalibai 929,000, inda sama da 624,000 daga cikinsu suka amfana da shirin.

Rahoton ya nuna cewa an amince da sabbin masu rejista 12,398, adadin da ya kai ƙarin kaso 1.4 cikin 100 idan aka kwatanta da rahoton baya.

Hukumar ta kuma bayyana cewa daga cikin kudaden da aka rarraba, An biya Naira Biliyan 65.3 kai tsaye ga makarantu 239 a fadin ƙasar a matsayin kudin makaranta, yayin da aka bada Naira Biliyan 51.1 ga dalibai a matsayin kudin walwala da abinci, jimillar kudin ya kama Naira Biliyan 116.4 zuwa yanzu.

A wani bangare na sanarwar, NELFUND ta bayyana bude sabon shafin neman lamunin karatu domin zangon karatu na 2025/2026, wadda za a bude daga Alhamis, 23 ga Oktoba, zuwa Asabar, 31 ga Janairu, 2026.

A cewar darektan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi, sabbin masu neman lamuni za su iya amfani da lambar shiga jami’a (admission number) ko lambar JAMB wajen cikawa, maimakon lambar dalibi (matric number).

Hukumar NELFUND dai an kafa ta ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa shirin lamunin dalibai a watan Afrilu 2024. Shirin yana bai wa daliban da ke karatu a makarantu na gwamnati damar samun lamuni ba tare da ruwa ba, domin biyan kudin makaranta da kuma samun kuɗin abinci yayin karatu.

Manufar shirin ita ce rage cikas na kudi da ke hana matasa shiga manyan makarantu da kuma bunkasa damar ilimi ga ‘ya’yan talakawa.

Ana sa ran daliban da suka ci gajiyar shirin za su fara biyan lamunin bayan sun sami aikin yi da zarar sun kammala karatunsu.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *