Kudin FAAC: Jihohin Arewa Sun Sami Ƙarin Kimanin Kashi 40 cikin Dari a Watanni Hudu na Farkon 2025

A rabon kudaden Kwamitin Raba Kudaden Shiga na Tarayya (FAAC) na zangon farko na shekarar 2025, jihohin Najeriya 36 sun raba jimillar Naira Tiriliyan 1.78, wanda in aka kwatanta da Naira Tiriliyan 1.27 da aka raba a zangon farko na 2024, an samu karin kashi 40% cikin dari.

Arewa maso Yamma ce ta fi samun ƙarin kuɗaɗen da kaso mafi girma daga Naira Biliyan 196.4 a Zangon Farko na 2024 zuwa Naira Biliyan 294.2 a Zangon Farko na 2025, ƙarin kaso 49.8% cikin ɗari. Arewa maso Gabas ta samu ƙari daga Naira Biliyan 177.3 zuwa Naira Biliyan 240.6, ƙarin kaso 35.7% cikin ɗari. Sannan Arewa ta Tsakiya ta samu ƙarin kaso 30.2% cikin ɗari, daga Naira Biliyan 196.3 zuwa Naira Biliyan 255.7.

Wannan cigaba ya biyo bayan irin sabbin matakai da tsare-tsaren da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ɗauka don inganta tattalin arzikin ƙasa, ƙarin kuɗaɗen shiga da kuma inganta rayuwar yan Najeriya a matakai daban-daban.

Ana sa ran gwamnatocin Jihohi Najeriya zasu yi amfani da wannan karin kudade wajen ƙara ingantattun hanyoyi, asibitoci, makarantu, ruwan sha da sauran abubuwan jin dadin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *