Ma’aikata Sun Bayyana Kwarin Gwiwarsu Ga Sabon Gyaran Harajin Gwamnatin Shugaba Tinubu Yayin da Albashin Su Na Janairu Ya Ƙaru

Ma’aikata a sassa daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin Nijeriya sun bayyana farin ciki da kwarin gwiwa biyo bayan raguwar kuɗin harajin da ake cirewa daga albashin watan Janairu na shekarar 2026, bayan fara aiki da sabon gyaran haraji da Gwamnatin Tarayya ta aiwatar a farkon shekarar nan.

Wasu daga cikin ma’aikatan da suka wallafa ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta sun tabbatar da cewa sabon tsarin harajin ya ƙara musu abin da suke samu na albashi, musamman ga masu ƙarami da matsakaicin albashi.

Mahmud Galadanci, ma’aikacin Banki, ya ce sauyin ya bayyana a cikin takardar albashinsa na watan Janairu.

“Tabbas sabon dokar haraji ya fi tsohon. Albashina ya ƙaru da N3,500 sakamakon rage haraji. Na gode, Mallam Tinubu,” in ji shi.

Shi ma Yarima Sulaiman ya bayyana sabon tsarin a matsayin babban sauƙi idan aka kwatanta da tsohon tsarin da ya ce yana da nauyi matuƙa.

“Ya fi sauki sosai fiye da baya. Muna fatan za a ci gaba da haka. A da ina biyan haraji kusan kashi 19.2, wanda ya kai sama da N300,000, amma yanzu ina biyan kusan N200,000,” in ji shi.

Haka nan, Hussain Spikin ya ce shima albashinsa ya ƙaru ƙarƙashin sabon tsarin.

“Na samu ƙarin N7,800,” in ji shi

Da yake bayani a matsayinsa na ƙwararre, Ado Mohammed Abubakar, PhD, wandƘwararren Akanta ne Mai Lasisi kuma Ƙwararren Masanin Haraji Mai Lasisi daga Kano, ya ce an tsara gyaran harajin ne domin samar da adalci da rage nauyin da ke kan ma’aikata masu rauni.

“Masu ƙarancin albashi sun samu ragi, masu albashi mai tsoka kuma sun ga ƙari idan aka kwatanta da abin da suke biya a baya,” in ji shi, yana mai ƙara bayyana cewa hakan na nufin an rage wa masu ƙaramin albashi haraji sosai, yayin da aka daidaita tsarin biyan haraji ga masu albashi mai yawa.

Tun da farko, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gyaran harajin na da nufin inganta walwalar ma’aikata, ƙara bin doka wajen biyan haraji, da kuma farfaɗo da tattalin arziƙi ta hanyar ƙara kuɗin da jama’a ke da shi a hannu.

Yayin da ma’aikata ke fara jin tasirin gyaran, da dama sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da dorewar wannan tsari tare da aiwatar da shi yadda ya kamata a dukkan sassa, suna masu fatan hakan zai haifar da daidaiton tattalin arziƙi da ingantacciyar rayuwa ga al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *